Abubuwa Shida 6 Da Ke Kashe Batirin Waya Android Ko Keyboard
Abubuwa shida 6 da ke kashe batirin waya android ko Keyboard.
Barkanku da zuwa wannan website namu mai albarbar wato Ginsau.com
A yau mun zo muku da abubuwan da suke kashe batirin waya babba ko karama; wato Android ko Keyboard.
ABUBUWA SHIDA 6 DA KE KASHE BATIRIN WAYA
BARIN CAJI YA YI KASA SOSAI
Barin cajin waya ya sauka har ya nuna alamar ja na kashe batirin waya. Wani lokaci ma yakan shafi kuzari ko hanzarin wayar. Yana da kyau batirin waya ta rika samun caji kamar yadda cikin dan Adam ke bukatar abinci da ruwan sha.
RASHIN SANIN LOKACIN CAJI
Yana da kyau duk mai amfani da waya ya san yanayi da lokutan da fi dacewa ya sanya ta caji. Misali a lokacin zafi waya takan fuskanci matsaloli, saboda zafi yakan sa cajinta saurin sauka. Don haka yana da kyau a rika sanya a caji da safe ko dare, lokacin da zafi ya ragu. Ko kuma a sa ta caji a wurin da yake da sanyi, hakan zai taimaka wajen hana mutuwar batiri.
BARIN RIGAR WAYA A JIKINTA ( COVER ) IDAN TANA CAJI
Waya kan dauki zafi a lokacin da aka makala ta a caji. Saboda haka, yana da kyau idan an sa caji a cire rigarta domin taimakawa wajen fitar zafin. Amma idan da rigar na jikinta, yakan hana zafin fita yadda ya kamata kuma zafin kan shafi batiri, wani lokaci har ya kashe shi.
YIN CAJI FIYE DA KIMA ( Over Charge )
A lokuta da dama masu amfani da waya kan sanya caji da dare, su kyale ta, har ta wuce kimar abin da take so. Ma’ana cajin da waya za ta yi cikin sa’o’i biyu zuwa uku, sai a bar ta ta kai sa’a takwas. Hakan na saurin kashe batirin waya.
ABUN CAJI ( CHAGER ) MARA INGANCI
Amfani da abubuwan cajin masara inganci na da tasiri wajen irin karfin cajin da batirin waya ke dauka. A wasu lokuta rashin ingancin abin jaci kan zama silar daina rike cajin waya.
BAMBANCIN BAKIN ABUN CAJI
Wayoyi sukan zo da bakin wajen caji iri-iri duk da cewa wasu za a ga kamarsu daya. Rashin amfani da bakin cajin da ya dace wajen cajin waya yakan taimaka wajen kashe batirin waya.
Wannan wasu kenan daga cikin abubuwan da ke kashe batirin waya.