Ya Password din ka yake? Ya kuma ya kamata a ce yake?
Assalamu Alaikum Barkanmu da sake saduwa daku cikin sabon cikin shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga howgist.com ya zama, Ya ka ke rubuta password dinka a akwatin Email din ka? Ko kuma na facebook ko kuma twitter da duk dai wani shafin internet da kake shiga. Idan har kai ma’abocin kokarin rubuta lambobi masu sauki ne kamar 123456, ko kuma 98654, ko kuma kana amfani da sanan suna ne wajen password din ka kamar salisu, Ibrahim, ko kuma kai mai son saka sunan masoyiyarka ne kamar Fatima, amrat, beebah ko Aisha, ko kuma kai ma’abocin rubutun kalmomin soyayya ne kamar iloveyou, ko kuma fatimamylove ko kuma thankyou, to ina tabbatar da cewar wannan password din naka zai zama mai sauki wajen ganowa ko bai zai yiwa hackers wahalar shiga ba domin sacewa ko kuma aika maka da virus cikin shafukanka ba.
Ga yadda ya kamata ka rubuta password dinka
Karanci harrufa goma (10)
Ya kunshi kananan harrufa da manya a cikin sa
Ya kunshi alamomin rubutun na musamman
Ya kasance lambobi a cikin su
Kada ya kunshi sunan masoyi, ko mahaifa da makamantansu
Kada ka yi amfani da sanannun kalmomi, kamar iloveyou, ihateyou, ihateu, da makamantansu
Kada kayi amfani da lamban wayarka ko na wani
Kada kuma ka yi amfani da ranar haihuwarka kamar, oct1977.
To ka yi la’akari idan ka kirkiri password dinka da wannan hada hade ya kake gani?