Makarantar Dan Sanda ta Jahar Kano Ta Fidda Sanarwa ta Daukar Sababbin Dalibai Na Wannan Shekaran 2024
Makarantar Dan sanda ta jahar Kano ta fidda sanarwa ta daukar sababbin dalibai.
Wannan makaranta da take a jahar Kano zata dauki sababin dalibai a daukar dalibai na 9 ga masu full time course.
Abubuwan da ake bukata wajen cikawa.
- Ana bukatar dalibi ya samu katin dan kasa wato NIN slip number.
- Ana bukatar dalibi ya kasance a tsakanin shekaru 17 zuwa 22.
- Ana bukatar dalibi ya samu credit 5 azaman jarabawar da be Gaza biyu ba sannan ya samu English da mathematics aciki.
- Ba’a bukatar masu aure ko wacce takeda da juna biyu su nemi wannan aikin.
- Ga Wanda suka Zama waec ko neco a 2017 dole ne suje da original result nasu.
Yadda za’a Yi apply.
- Za’a biya kudi kimanin dubu biyu ta cikin website na makarantar www.polac.edu.ng za’a je ayi generate na remita sannan abiya.
- Bayan an biya kudin za’a koma website na makarantar ayi verify na payment sannan a cire application slip Wanda za’a ga Rana da lokacin da za’a je aptitude test.
- Za’a Yi aptitude test ne daga 17 September zuwa 25 September 2022 kowa zai je da application slip daya fitar a cape.
- Ana bukatar kowa yaje da wadannan abubuwan Wajen aptitude test domin za’a Yi screening nasa, abubuwan sune kamar haka:-
. Dukkan Takardun makarantar da aka Gama. - Takardar shedar haihuwa data jaha data Dan kasa.
- Takardar sa hannun wani me mukamin kamar soja, Dan sanda, ko likita dasauransu Wanda yake da matsayin aiki me lamba G-12
- Sa hannu daga kotu ko police station Akan kyakykyawan dabi’a.
- Takardar asibiti ta shedar lafiya.
Aptitude test:
Za’a gudanar da aptitude test ga dukkan Wanda ya cike a cikin ICT na cikin makarantar.
Courses din za’a iya nema da Kuma facaulty nasu, akwai facaulty uku
Humanities, sciences da social sciences.
Ga masu neman humanities akwai department kamar haka:-
- English
- History and international relations
- Linguistics
Facaulty of sciences
- Biochemistry
- Biological sciences
- Chemistry
- Computer science
- Forensic science
- Mathematics
- Physics
Facaulty of social and management sciences.
- Accounting
- Economic
- Political science
- Psychology
- Sociology.
Tsawon lokacin Karatu
Wannan makaranta ta tsara tsawon lokacin shekaru biyar Ana karatu Wanda idan an Gama za’a samu matsayin assistant superintendent of police II ( ASP).
domin karin bayani ku tuntuni me kula da ayyukan makarantar na yanar gizo ta wannan number 09166611162
Muna muku fatan nasara
Also Read: Za’abawa Matasan Nigeria Training Akan Cyber Security