Advertisment
Tech & Guide

Yadda Za Ka Maida Kayan Tsohuwar Wayarka Zuwa Sabuwa Wayarka Cikin Sauƙi.

Sponsored Links

TRANSFER OLD PHONE TO NEW PHONE
Yadda Za Ka Maida Kayan Tsohuwar Wayarka Zuwa Sabuwa Wayarka Cikin Sauƙi. Kamar Su Applications, Messages Contacts, Call history Music, Videos, Games, da dai sauransu.

Barkanku da zuwa wannan website namu mai albarbar wato hasnice.hikimatv.com

Sau tari ba kowa bane yakeda sha’awar rike waya kala kala ba wani idan ya siya waya sai tayi masa sama da shekara biyu a hannunsa bai canza wata ba , sau tari kuma bawai saboda babu kudin canzawar bane A’a kawai saboda ya loda ma wayarsa abubuwa sosai kuma baya son ya rasasu musamman messages na wayar da sauran muhimman abubuwan da ya zuba ma wayar wanda canza wayar zaisa dole ya rasa wasu abubuwan a ciki.

To ga hanya mafi sauki da zakayi Transfering duk wani abu dake cikin tsohuwar wayarka zuwa sabuwar wayar da kasiya kamar irinsu :

 • Contacts ( Contact Phone Numbers )
 • Messages
 • Call history
 • Applications
 • Music
 • Videos
 • Games, da dai sauransu

Duk zasu sauka kai tsaye zuwa ga sabuwar wayar da ka canza insha Allah .

YADDA ZA KA MAIDA KAYAN TSOHUWAR WAYARKA ZUWA SABUWA WAYARKA CIKIN SAUƘI

Matakin farko idan sabuwar wayar babu Xender a ciki sai katura mata xender , daganan sai kashiga cikin xender din , itama haka zalika tsohowar wayar naka sai kashiga cikin xender dinta.

A cikin xender na sabuwar wayar naka daga gefen dama zakaga wata alama da take daga ƙarshe kusa da wata alama mai kamar alamar ‘ whatssp ‘ kana dannata zata bayyanar maka da wadannan abubuwan kamar haka :

 • Connect PC
 • Connect KaiOS
 • Scan Connect
 • Share Xender
 • Phone Copy
 • ga hotonshi nan a kasa

Sai ka danna wurin da aka rubuta ” Phone Copy ” kana dannawa zai bude maka daga cen sama zakaga wurin da aka rubuta ” Import All data from your old phone to the new one . ” sai kayo kasa zakaga wurin da zasu tambayeka shin wannan wayar sabuwar ce ko tsohuwar ?

To tunda a sabuwar ne sai ka danna wurin da kaga an rubuta ” New ” haka zalika itama tsohuwar wayar sai kayi Exactly kamar yadda kayi a sabuwar amma ita idan kazo wurin sai ka dannan ” Old ” ma’ana tsohuwar wayar kenan.

Kana danna alamar ” New” a sabuwar wayar naka ka tabbatar masu da cewa wayar itace sabuwar daganan zasu baka wani Options da zasu tambayeka shin ita tsohuwar wayar naka ” Android” ce ko ” Iphone ” idan Android ce sai ka danna wurin android , kana dannawa zasu bude maka wani shafi da zasu sanar dakai cewa ka tabbatar ka saka Application din xender a tsohuwar wayar naka domin da ita ne za’ayi aikin , to kuma daman kai Already kasaka sai kawai kayi kasa zakaga wurin da aka rubuta ” Next ” sai ka danna shi zai fara Processing zai nau’in maka da alama ta ” Scanner Pattern ” wato wanda zakayi scanning da tsohuwar wayar naka .

Ita kuma daman tsohuwar wayar naka kana tabbatar masu da itace tsohuwar zasu baka damar kayi scanning a sabuwar wayar daganan bayan tagama scanning shikenan sai tafara Transfering kayanka cikin wasu lokutta insha Allah zakaga komai ya sauka a tsaye kai tsaye babu bata lokaci .

Idan ba ka fahimci wani abu ba ka yi join a group ɗinmu na WhatsApp dake nan ƙasa domin tambaya. Allah Ya taimaka.

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button