Sabuwar Labarin Yajin Aikin ASUU
Kungiyar mallaman Jami’o’i na nigeria wato ASUU ta yanke shawarar ci gaba da yajin aikin da takeyi
Manyan jaridu a nigeria da ma kasashen ketare sun rawaito cewa matakin yazo ne Bayan wata zazzafar tattaunawa da akayi a ranar litinin Game da yadda Za’a cimma matsaya tsakanin kungiyar da Kuma gwamnati
An dauki matakin ci gaba da yajin aikin bayan ganawar kwamatin zartarwa a hedikwatar ASUU dake jami’ar Abuja, babban birnin tarayyar nigeria
Kungiyar ASUU dai ta shafe sama da wata 6 tana gudanar da yajin aikin da ya tilastawa Dalibai zaman gida
ASUU na ganin gudanar da yajin aikin ne hanyar samun Mafita ga tarin bukatun da ta gabatarwa gwamnatin nigeria ciki har da batun inganta musu albashi
Also Read: Sabuwar Sanarwar Ga Wanda Suka Cika Karbar Horo Da Gasa Na Cyber Security