Attajirin duniya Elon musk ya dauki alkawarin kawo matsalar data a Nigeriya.
Attajirin duniya Elon musk ya dauki alkawarin kawo matsalar data a Nigeriya.
Kamar yadda kowa ya sani Elon musk Dan kasar America shine Wanda a yanxu ya fi kowa kudi a duniya,
Wannan kasurgumin me kudi ya dauki alwashin kawo matsalar data data addafi mutane Yan kasar Nageriya.
Kowa ya san amfanin data ba Sai mun bayyana yadda miliyoyin mutane ke kashe kudi Wajen ganin sun siyi data ba a wannan kasar duba da yadda take da tsada gashi Bata da auki sannan ga barazanar Kara Mata kudi da kamfanonin sadarwa suke a kullum..
Wasu na amfani da data ta hanyar kasuwanci wasu Kuma sunayi ne domin nishadi wasu Kuma ta hanyar social media dasauransu.
Elon musk yayi wannan alkawari ne na kawo karshen wannan matsalar ta data dake addabar Yan kasar Nageriya Wanda a halin yanxu ya samu lasisin yarjewa daga hukumar Nigerian Commission Commission wato NCC wannan hukuma ce me kula da layikan sadarwa ta kasar nigeria.
Wannan me kudin duniyar Elon musk Yana da wani gagarumin kamfanin sadarwa Wanda ake amfani dashi a kasashen turai me suna Starlin network Kuma yanxu ya samu lasisin Fara Aiki a kasar Nageriya, wannan kamfani ya shahara a kasashen turai Kuma kamfanin sadarwa ne daya ke da saukin amfani dashi.
Akwai hasashen wannan kamfanin na Starlin network zai Zama gagara gasa ga dukkan kamfanin sadarwa da ake da su a kasar Nageriya kamar su MTN, Airtel, Glo da 9mobile.
Muna fatan zuwan wannan kamfanin sadarwa ya kawo Mana cigaba sauki da garabasa a wannan kasa ta Nigeriya.