Kannywood
Duk namijin da ya ke barin matarsa tana rawar TikTok ba zai ji kamshin Aljannah ba –Rukayya Dawayya
Sponsored Links
Jaruma Rukayya Dawayya a wani bidiyo da ta yi wanda
Hadiza Gabon ta wallafa a shafinta na Facebook ta ja
hankali ga mata musamman masu aure da su ke raye-raye
a shafukansu na TikTok.
Jarumar ta fara ne da bayar da wani labari takaitacce wanda
ta ce ya auku da ita a lokacin tana da aure.
Jarumar ta fara da bayyana yadda wasu shakikan kawayenta
su ka kai mata ziyara gidanta da ke Abuja bayan ta ci
kwalliya amma mijinta bai gani ba.
Tana samun labarin sun kai mata ziyarar tace a sanar
dasu cewa bata nan duk don kada su ga kwalliyarta kafin
mijinta ya gani
A cewar jarumar, har sai da mijinta ya dawo ya ga kwalliyar
sannan daga bisani ta kira su ta ce musu ta dawo daga inda
ta je. sannan suka Zo suka hadu
Daga karshen bidiyon tace duk macen da ke yin kwalliya ta
wallafa bidiyon kwalliyar ta a shafin TikTok bata son mijinta, yayin da
mazan da su ke barin matansu su na bidiyon ba sa kaunar
matan kuma basa kishinsu.
Jarumar ta ce ko kamshin Aljannah namiji mara kishi ba zai
ji ba, saboda hakan fadin manzon Allah (SAW) ne.
Ta ce da ace mata za su ga wasu mazan da ke kallon
bidiyonsu na TikTok da ba su yi ba tun farko da har kuka sai
sun yi.
A cewar jarumar, “Duk macen da ta ke son mijinta tana
killace kanta ne tare da boye surar jikinta, mijinta kadai za ta
bayyana wa su.”
Jarumar ta kara da cewa duk namijin da ya ga bidiyon matar
aure a TikTok ba zai so ya kara gani ba saboda shi ma ba
zai so ta shi ta yi bidiyo irin wannan ba.
Daga karshe jarumar ta yi addu’a inda ta ce Allah ya yi
mana maganin bala’in da ya shigo, wai shi TikTok.
Da fatan masu yi za su kiyaye kuma su ji wa’azin nata da
kunnen basira.
sai muce
Allah ya gafarce mu.
Sponsored Links