Advertisment
Education

Jami’ar prince Abubakar Audu Anyigbe dake jahar kogi ta sanar da ranar da zata Fara gudanar da Post-utme screening

Sponsored Links

Jami’ar prince Abubakar Audu Anyigbe dake jahar kogi ta sanar da ranar da zata Fara gudanar da Post-utme screening.

Wannan jami’a dake jahar kogi wacce ake Kira prince Abubakar Audu ta sanar da ranar da zata Fara gudanar da Post-utme screening na wannan shekaran Wanda za’a Fara daga Monday awatan August ranar 22 zuwa Saturday goma ga watan September shekara ta 2022.

Mafi karancin Makin da ake bukata a wannan makaranta shine 140 Amma akwai department din da nasu yafi haka sannan ga dukkan masu sha’awar Shiga makarantar ya Zama dole su biya kudin screening kimanin naira 2000.

Ga masu son Shiga wannan makaranta da Jamb ya Zama dole su kasance suna da wadannan abubuwan kamar haka:-

  1. Ya Zama dole ga Wanda suka son Shiga wannan makaranta ya Zama sun cike ta a first choice nasu na Jamb.
  2. Dole ne Wanda zasu nemi wannan makaranta ya Zama suna da maki akalla 140 sannan ya Zama suna da kyakykyawan combination a jamb nasu.
  3. Dole ne yazama suna da credit biyar a neco ko waec ko nabteb Wanda ya hada da English mathematics da sauran course Wanda suka danganci suka danganci department din za’a karanta.
  4. Ya Zama dole su dalibi ya Dora credentials nasa a shafin Jamb.
  5. sannan ga Wanda result nasu be shiga hannu ba zasu zabi AR ma’ana awaiting result sannan duk lokacin daya Shiga hannu zasuje jamb office mafi kusa dasu su Dora a dashboard nasu na Jamb.

Yadda zaku nemi wannan makaranta.

  1. An bukaci daliban dasu Shiga shafin makarantar Wanda yake kamar haka www.ksuportal.edu.ng sannan su biya adadin kudin kimanin dubu buyu, idan baza iya da kanka ba zakaje kafe mafi kusa dakai su ma..
  2. Dole ne daliban su bayyana sakamakon jarabawar su ta SSCE ga masu Jamb data A’level ga masu D.E wato makarantar dasuka Bari ta NCE ko Diploma ko IJMB dasauransu, Ana bukatar su cike kome ba tare da kuskure ba.
  3. Bayan Nan Ana bukatar su duba dukkan abinda Suka cike kafin suyi submit na application nasu.

Ga daliban da zasu nema da Direct entery D.E wato Wanda zasu Fara daga 200 Level.
Ana bukatar Wanda zasu nema da d.e dasu bi Hanyoyi da aka fada Asama na masu nema da jamb. Wato suna dole Sai sun cike jamb Amma su ba’a rubuta Jamb kawai form ake saya Sai a zabi makarantar da ake son zuwa.

Za’a Fara screening ne daga Monday 22 August zuwa 10 ga watan September shekara ta 2022.

Ana sanarwa da daliban da zasu nema dasu fidda slip Wanda dashine zasuje Wajen post utme screening yayin da suka gama online application.
A wannan slip zasuga date da Kuma ranar da zasuje screening din.

Cikewa wannan makaranta zai Fara ne daga 20 ga watan July zuwa 20 August shekara ta 2022.

Ya Zama dole ga dalibai dasu halarci Wajen post utme examination da face marks sannan su bada tazara yayin gudanar da wannan jarabawar.

Domin Karin bayanai kalli hoton dake kasa.

Muna muku fatan nasara

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button