Kungiyar Mallaman Jami’o’i Ta Nigeria Sun Kara Wa’adin Yajin Aikin Da Sukeyi
Kungiyar mallaman makarantar jami’o’in nigeria wato ASUU ta Bayyana aniyarta na sake Kara wa’adin yajin aiki da sukeyi a yanzu
Kungiyar ASUU dai ta sake Kara wa’adin mako hudu akan sauran kwanakin da tayi tana yajin aiki
Wanda Daman tuni dai kungiyar ta ASUU ta Jima tana yajin aiki Wanda a yanzu idan har kungiyar tayi mako hudu din Nan Bata koma bakin aiki ba tayi wata shida kenan Tana gudanar da yajin aiki Wanda lissafin wata shida yayi dai dai d Rabin shekara
Sanarwar hakan ta hannun shugaban kungiyar Emmanuel osodeke, an Kuma fitar da ne Bayan kammala wani Dan karamin zama na gaggawa da wasu manyan kungiyar sukayi a ranar lahadi birnin tarayya Abuja
Kazalika ASUU ta godewa kungiyar kwadago ta NCL, dama sauran kungiyoyin da suka Mara Mata baya wurin yin zanga-zangar nuna goyon baya da nufin kawo karshen yajin aikin.
Kungiyar ta kara dacewa ta tsawaita yajin aikin ne da mako hudu,saboda ta Lura cewa har yanzu gwamnatin nigeria Bata nuna wata alama ta kawo karshen zaman Dalibai a gida ba.
ASUU dai ta Shiga yajin aiki tun ranar 14 ga watan February 2024 ta tsunduma yajin aiki,bisa zargin Gwamnatin nigeria da gaza cika alkawarin da ta daukawa kungiyar cikin alkawarin kuwa sun da, batun inganta rayuwar mallaman Jami’o’i tare da dambarawar shigar da kungiyar tsarin biyan albashi na IPPIS da Gwamnatin ta fito d shi.