Advertisment
News

Gwamnatin Nigeria Ta Kashe Naira Tiriliyan Biyu Wajen Tallafin Man Fetur

Sponsored Links

Gwamnatin nigeria ta kashe naira tiriliyan biyu wajen biyan kudin tallafin man fetur cikin wata shida na shekarar 2022, acewar rohoton Kamfanin Mai na kasar NNPC.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa a ranar talata ne NPPC ya gabatar da rohoton ga kwamatin asusun kasafi na kasa wato Federal Account Allocation Committee (FAAC)

Saboda Karin yawan kudin da ake biya na tallafin yasa NPPC Bai Bai wa gwamnatin kasar ko kwandala ba a matsayin riba cikin shekarar Nan a cewar rahoton,

A shekarar da ta wuce gwamnatin na biyan naira biliyan 100 ne duk wata a matsayin kudin tallafin. Shugabannin Kamfanin basu ce komai ba lokacin da Reuters ya nemi Karin bayani.

A watan janairu ne ya Kamata kasar ta dakatar da biyan tallafin Amma sai gwamnatin shugaba Muhammad buhari ta dage matakin, tana Mai cewa nauyin zaiyi was Yan kasar yawa yayin da ake fama da hauhawar farashi.

Nigeria na shigar da dukkan man fetir din da ake amfani da shi a kasar saboda matatar Mai da ke cikin gida basa aiki.

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button