Minene Gaskiyar Sakon Da Ake Aikowa Daga National Social Empowering Scheme In Nigeria Wato NSEIP
Kamar ba’a Dade ba mutane da dama suka cike wannan Shirin na National social Empowering Scheme In Nigery NSEIP.
Wannan Shirine na Gwabnati tarayya ta fitar domin tallafawa matasa marasa galihu da masu zaman banza domin su dogara da kansu.
A kwanakin Nan mutane da dama sun samu sakon cewa sun samu shiga Wannan shirin na National social Empowering Scheme In Nigery wato NSEIP wadda aka bukaci dasu tura kudi kimanin naira 850 Wanda aka Basu zabin da suje POS ko suyi transfer ta WEMA bank domin su tura wannan kudin.
Sannan a wannan sakon an bukaci da su saka kudin aranar kada ya wuce karfe 5pm na yamma sannan Bayan sun biya kudin sun saka wani link Wanda zasubi ta Nan domin su Sami receipt na kudin da suka biya sannan wannan receipt zasu je Wajen training dashi ranar 14/07/2022.
Ya kamata kowa yasani wannan sako be fito daga hukumar National social Empowering Scheme In Nigery wato NSEIP ba don haka kada kowa ya kuskura ya tura kudi domin macuta ne.
Muna Kara sanarwa mutane dasu guji irin wanann sakonnin domin macuta ne.
Online scammers sunyi yawa a online domin hakan ya kamata mutane a kiyaye inde wani tallafi ko bada horo Wanda ya fito daga Gwabnatin tarayya baza’a taba tambayar Sai an biya kudi ba yakamata ku San hakan.
Allah ya Kara kiyayewa
Also Read: Hukumar Wutar Lantarki Ta Fitar Da Shortlist Na Wanda Sukayi Nasarar Samun Aiki