Advertisment
Education

Takalifi da Karin Haske Akan Littafin JAMB 2024, The Life Changer daga Muhd Nura Sallau Yarganji

Sponsored Links

Cikakken bayani da sharhi da ƙarin haske da Summary na taƙaitaccen labarin da Jigon (Themes) da ‘yan wasa na littafin JAMB, The Life Changer (Jalli’s 1st).

✍️ : – Muhammad Nura Sallau Yarganji

Littafin the Life Changer an fara bugasa ne a shekarar 2020, na Khadijah Abubakar Jalli, Littafin ya kawo labarin da Ummi Ahmad ta bawa yaran ta na abin da ya faru loƙacin tana Digiri na farko da wata daga cikin Course Mate ɗin ta Salma.

Hukumar shirya jarrabawar makarantun gaba da Secondary wacce akafi sani da JAMB, ta zaɓi littafin the Life Changer na Mallama Khadijah Abubakar Jalli, a matsayin littafin da zatai amfani da shi kamar yadda hukumar ta saba.

Hukumar ta ɗauki littafin ne bayan dubawa da tantace littafin, sannan littafin yana da kyakkyawar manufa da isar da cikakken saƙo ga makaranci, musamman ɗalibai, ta yadda marubuciyar tayi amfani da rayuwar makaranta a littafin, wanda hakan yasa ta isar da saƙo mai mahimmanci ga ɗalibai musamman masu son shiga makarantun gaba da Secondary.

Marubuciyar ta raba littafin zuwa Chapter-Chapter, means babi-babi har zuwa kaso tara. Sannan tayi amfani da ‘yan wasa (Characters) kamar haka :

  1. Ummi Ahmed : – Itace babbar ‘yar wasa a labarin itace ta bawa yaran ta labarai mahaifiyar yara huɗu
  2. Bint : – Bint ita ce ‘yar auta a yaran Ahmed sannan kuma ‘yar shekara biyar, itace ta yiwa Malamin Social Studies ɗin su tambaya akan French bayan shima yayi tambaya ta bashi amsa.
  3. Mallam Salihu : – shine Malamin Social Studies a makarantar su Bint, wanda ta tambaya akan French ya fice daga ajin.
  4. Jamila : – Itace yarinya ta uku sannan ta biyu a mata, cikin ahalin Ahmed mijin Ummi.
  5. Teema : – itace yarinya ta biyu sannan ta ɗaya a mata cikin ‘ya’yan Ahmed.
  6. Umar : – Matashin yaro ne ɗan shekara 18 mai iya kwalliya da sanya tufafi mai kyau, jarrabawar sa ta SSCE da JAMB abar yabawa ce sosai, ya samu admission a Jami’ar Ahmadu Bello domin yin karatun Shari’a (Law).
  7. Talle : – An haifeshi a ƙauyen Lafayette sannan mahaifin sa da matar mahaifin sa sun yi hatsari, shine wanda ya haɗa hannu da su Zaki sukai Kidnap ɗin wani yaro domin ya samu kuɗi.
  8. Salma : – Matashiya ce doguwa siririya wacce aka kora a Jami’ar su tana aji 400 saboda satar jarrabawa.
  9. Tomiwa : – Musulma ce daga Ibadan tana son Entertainment, sannan ta na daburin zama mawakiya.
  10. Ada : – Ada ‘yar Benue ce ɗakin su ɗaya da Salma a makaranta.
  11. Ngozi : – Ɗakin su ɗaya da Salma ita ‘yar Imo ce tana da sauƙin kai sannan idan zata girka abinci bata girkawa ita kaɗai.
  12. Habib : – Ɗan siyasa ne sun haɗu da Salma a Kwangila, sannan suka rage mata hanya zuwa Jami’a da shi da abokin sa Labaran.
  13. Labaran : – Babban aminin Habibu ne tun na yarinta sanda Habib yana makaranta Labaran yana ɗan taimaka masa da ɗan wanin abun, bayan Habib ya zama ɗan siyasa sai ya zaɓi Labaran ya zama Direban sa.
  14. Zaki : – Shine yazo da tunanin yin garkuwa da ɗan abokin sa domin ya samu kuɗin fansa ya haɗa hannu da Talle saboda Talle yana matuƙar buƙatar kuɗi a loƙacin.
  15. Dr. Samuel Johnson : – Matashin Lakcara ne a Department ɗin su Ummi sannan ya taimake ta sosai wajan naiman Admission, kuma aminin mijin Ummi ne.
  16. Dr. Dabo : – Malamine mai iya bayar da tarbiyya, sannan baya huɗɗa da ɗalibai mata kuma ba’a zuwa gurin shi bayan Lakca, sannan yana koƙarin yin adalci tsakanin ɗaliban sa, shine wanda ya buƙaci Salma ta zama Friend ɗin sa.
  17. Hakimi : – Shine Hakimi Lafayette wanda ‘yan sanda suka kama Talle a gidan sa.
  18. Kolawole Abdul : – Abokin karatun Salma ne ajin su ɗaya yana da ƙoƙari sosai, shine garin taimakawa Salma aka kamashi aka kore shi daga makarantar.
  19. Muhammad Kabir : – Shi ne Dr. Kabir ba Malamin Jami’ar ne ba sannan shine Shugaban Kwamitin EMEC.
  20. Lawal : – Abokin Salim ne wanda yaƙi yarda ya rakashi gurin budurwar sa, suka haɗu a Social Media.
  21. Natasha : – Ita ce budurwar da suka haɗu da Salim a Social Media.
  22. Salim : – Shine saurayin da suka haɗu da Natasha a Social Media.
  23. Kartagi : – Shine jagoran gurin cacar da Muhammadu Kabir yake zuwa caca.
  24. Gumusu : – Shine wanda aka tura bayan Muhammadu Kabir.

Taƙaitaccen Labarin

Labari ne mai daɗi da daɗin karatun da kowanne ɗalibi zai ji daɗin sa. Labarin Salma da rayuwar ta da ƙawayen ta Campus.

Littafin a taƙaice (Summary) na littafin.

Labarin ya soma ne da gurin da Bint yarinya ‘yar shekara biyar, wacce take acikin ‘yan uwanta kuma ahalin ta suna son ta, inda Bint take basu labarin makarantar su, da yadda ta kaya tsakanin ta Mallamin su Mallam Salihu akan French, ta bashi amsar yaya zata ce “Good Morning ” sannan ita kuma ta tambaye shi yaya zata “That’s very good ” da French duk da kasancewar Malam Salihu yana ji da kansa a ilimi, sai da ya gaza iya bata amsa, hakan yasa ya fuce daga ajin su Bint, kuma bai dawo ba sai bayan Break ya bata amsa da taimakon Malamar French, sai Ummi tace musu su yabawa Malam Salihu akan abin da yayi na ƙin bawa Bint amsar abin da bai sani ba har sai da ya tambayi Malamar French, suna cikin wannan hirar sai kuma Umar yayan Bint ya shigo, Umar yayan Bint ne sai ya shigo da kyakkyawan labarin ya sami admission a Jami’ar Ahmadu Bello zai karanci Law, kasan cewar zuwan Umar da kyakkyawan Labarin samun gurbin karatu a Jami’ar, hakan yasa mahafiyar ta ga yakamata ta bashi wasu daga cikin labaran loƙacin tana Jami’a daga ciki harda labarin Salma da abokan ta na ɗaki a Jami’a, mahafiyar Umar ta soma bashi labari ne tun daga barin ta kauyen su na Lafayette zuwa Jami’a bayan ta bi sharaɗin babanta nayin aure kafin soma zuwa Jami’a kuma mijin nata ya amince. Sanna Ummi ta bawa Umar labarin loƙacin da taje registration Na Department dana Faculty, wanda daga ƙarshe har ta haɗu da wani Dr. Samuel Johnson wanda yake ba musulmi bane shi, sai daga baya mijin ta yake gaya mata Dr. Samuel Johnson abokin sa ne kuma shine ya taimaka masa wajan samun admission ɗin ta, ta cigaba da bawa yaran nata labari har labarin inda ta haɗu da Salma.

Ummi ta bawa Umar labarin Talle, Talle an haifeshi a Lafayette mahafiyar sa ta mutu bayan haihuwar sa, sannan kuma ya rasa mahaifin sa da matar mahaifin sa yana da shekara 20, an sanar da Hakimi loƙacin da aka ga Talle yan siyayya fiye abin da yake siya a baya, bayan Hakimi ya kirashi domin tuhumar sa Talle ga gaza amsa tambayoyin da Hakimi yayi masa, ana cikin haka sai ga ‘yan sanda nan sun zo gidan Hakimi suka kama Talle, sannan suka gayawa Hakimi Talle yana Kidnappings ne, suka je gidan Talle ya nuna musu inda ya ajjiye wanda yayi Kidnap, sannan aka yankewa Talle da Zaki hukuncin zama gidan yari. Salma wacce take ɗaliba a Jami’a. Dr. Dabo Level Coordinator ne na ‘yan Level one, yana da yin adalci tsakanin ɗalibai, wanda Salma taƙi amicewa da zama Friend da Dr. Dabo hakan yasa Dr. Dabo baiji daɗin hakan ba,

Salma ta sami ɗakin Queen Amina duk da cewa farko bata son roommate ɗin nata Ada, Tomiwa, da Ngozi, amma daga ƙarshe sai da suka zama kamar ‘yan uwa. Salma ta haɗu da Habib da Labaran suka rage mata hanya daga Kwangila zuwa makaranta, bayan sun sauke ta tace musu sunan ta Tomiwa ta kuma basu lambar Tomiwa, kashegari Habib ya kira Tomiwa yace suna kofar Hostel ɗin su, bayan ta futo ya gane ba ita bace daga ƙarshe ya bata 50k, yace ta bawa roommate ɗin ta 10k kowacce sannan ta riƙe 20k, Habib da Labaran abokai ne tun yarinta loƙacin da Habib ya tafi makaranta sai Labaran ya tafi Driving School Labaran ya taimaki Habib loƙacin da yana makaranta da ‘yan abubuwan da ba za’a rasa ba, sannan bayan Habib ya zama ɗan siyasa sai ya mayar da Labaran Direban sa.

Bayan an dawo makaranta duk da kasancewar ‘yan matan suna kula samari amma hakan bai taɓa karatun su sosai ba, domin da alamu duk zasu futa da Upper Second Class, kasancewar Course ɗin Moral Philosophy mai sauƙi ne Salma bata halartar Lectures ɗin Malamin, saboda taga duk kusan shekara mai maita tambayar ake, shiyasa tafi himmatuwa da karanta Past Q, bayan Salma ta shiga ɗakin Jarrabawar sai ta gano ba haka bane Malamin ya sauya hakan ne yasa ta kama naiman wanda zai taimake ta, sai da kyar ta samu Kolawole Abdul, sai kuma Invigilator ta kama su, Salma tana kwafar rubutun Kolawole Abdul, Malamar ta sanya su suka cike Form ɗin satar amsa EMIL FORM sannan ta sanya na kusa da su suka sanya hannun a a witness, daga ƙarshe aka kori Salma da Kolawole Abdul. Salma ta buƙaci ƙawarta Tomiwa da ta sanya su Habib da Labaran su tallafa mata wajen futa daga wannan iftila’in Habib yace mutum ɗaya kawai ya sani Prof. Dabo, amma kuma sai Salma ta tuna shine wanda taƙi yarda ta zama Friend ɗin sa tun a Level 1, daga nan sai Salma ta buƙaci Habib ya taimaka mata da wasu ‘yan kuɗaɗe da zata bawa Dr. Muhammad Kabir domin shine shugaban EMEC kwamitin ɗin, kuma har imanin sa zai iya siyarwa akan kuɗi, sai Salma ta tsara haɗuwa da shi a Hotel, domin tunkarar shi da batun, sai daga baya Salma ta gane Dr. Muhammad Kabir ba Dakta bane kawai dai suna ne abokan sa suke gaya masa shi kawai Laboratory Technician ne a makarantar daga nan sai ta gayawa Labaran shi kuma yasa Zaki ya tursasa Dr. Muhammad Kabir akan ya dawo da kuɗin da Salma ta bashi, domin dama su Habib sun san Zaki domin Habib ne yasa shi ma yayi Kidnap na yaron Alhaji Adamu. Sannan kuma sai Ummi ta rufe musu da labarin saurayin Salma, Salim wanda ya haɗu da Natasha tayi koƙarin yaudarar sa, sai ya gano ta daga baya tana da haɗin kai da Kidnappers.

Ummi ta bawa yaran ta wannan labaran ne, domin ya zama wa’azi a gare su musamman Umar da yake shirin tafiya Jami’a yanzu.

Cikin abubuwan da ta wa’azantar da Umar ta hanyar Labarin, sun haɗar da ya kula da abokai a makaranta yasan da suwa zaiyi abota ta hanyar labarin Salma, sannan yaguji abokan da zasu ingiza shi ga shiga Cultism da Exam Malpractice.

Jigon Labarin.

Kamar yadda kowa yasani akwai Jigo a cikin kowanne labari, musamman masu karanta littafin na, ko rubutun ko Programs ɗina na Literature In English, akwai Jigo, to haka zalika wannan littafin na Mallama Khadija Abubakar Jalli shima yana da Jigon sa, ga wasu daga cikin Jigon littafin :

  1. Rabe-raben dake cikin ƙasa da haɗin kai (National Diversity And Unity).
  2. Youthfulnes (rayuwar matasa).
  3. Cin hanci da rashawa (Corruption).
  4. Abu mai kyau da alkhairai (Goodness).
  5. Adalci (Justice).
  6. Tasirin alaƙar kafafen sadarwar zamani (Social Media Relations).
  7. Addinai (Religions)

Mallama Khadijah Abubakar Jalli dai ta kasance tana da Digirin Bachala akan lissafi (Mathematics), sannan kuma tana kasuwanci, kuma itace ta samar da She’s Boutique Africa, kuma tana da aure sannan Allah ya azurtata da ‘ya’ya.

Alhamdulillah!

Muhammad Nura Sallau Yarganji
1st Winner Prize Of 2021 Writers Competition.
National Director General Of Media, Publications & Publicity
Arewa Students Orientation Forum.

Friday 3rd January 2023.
11:00 AM.

© ASOF_2023
WHATSAPP
08086251045

Also Read: Hukumar Civil Defense Ta Fitar Da Sanarwa Yau

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button