Advertisment
Education

Yadda zaku duba sakamakon jarabawar ku ta jamb.

Sponsored Links

Yadda zaku duba sakamakon jarabawar ku ta jamb.

A yau ne hukumar shirya jarabawar Shiga jami’oi wadda akafi sani da joint Admission and matriculation board Jamb ta sanar da fitowar sakamakon na Jarabawar ga daliban da suka zana jarabawar a Wannan Shekaran ta 2022 wacce ta gudana satin daya wuce.

Fabian Benjamin shugaban shugaban Hulda da jamb shine ya bayyana fitowar sakamakon na Jarabawar ta Jamb shine ya saki bayanin fitar sakamakon na jamb a yau asabar 14 may 2022 Wanda gidan jaridar The Nation ta ruwaito.

A halin yanxu duba wannan sakamakon na Jarabawar jamb hanya daya ce tilo wacce dukkan Wanda ya rubuta jamb sannan yake son duba sakamakonsa zai bi domin ganin abinda ya samu.

Hanyar de itace dole ne Wanda yake son ganin sakamakon nasa na jamb ya nemi sim card wato Layin wayar da yayi register jamb da ita domin da ita ne kawai zai iya duba wannan sakamakon nasa.

Yadda zaku shine kuje message na wayar ku saiku rubuta da manyan Baki wato Capital letters UTMERESULT zuwa 55019 zasu ciri kudi kimanin naira 50 kafin su Nuno muku sakamakon naku saboda haka dole ne ku tabbatar akwai kati acikin wayar ku kafin ku aika sakon.

Hukumar ta Jamb tace wannan ce hanya daya tilo ta duba sakamakon jarabawar sabanin yadda aka sani a lokutan baya Ana dubawa ne ta cikin website na Jamb, saide sun tabbatar Nan kusa zasu Dora sakamakon kowa a cikin website kamar yadda aka saba.

Muna muku fatan nasara.!

Ziyarci shafinmu na.

WhatsApp group 1

Facebook page

WhatsApp group 2

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button