Advertisment
Policy

Yadda zakuyi da tsofaffin kuɗaɗen ku..

Sponsored Links

Yadda zakuyi da tsofaffin kuɗaɗen ku..

Ka’idojin yadda ake kai tsofaffin takardun kuɗi a babban bankín CBN

  1. Idan ka kai kudin ba za a chanza maka da sababbi ba, sai dai a saka maka acikin asusun ajiyarka na banki (Account)
  2. Hukuma zata bincika ta tabbatar da cewa asusun ajiyarka baya da wata matsala, kamin asaka maka kudin, idan aka fahimci akwai damuwa ga asusunka na banki, to za a dawo maka da kudinka.
  3. Wani ba zai kai kudin wani ba. Kowa shi zai kai kudinsa da kansa kuma asusun ajiyarsa na banki zai bayar a saka kudin aciki.
  4. Kamin ka tafi bankin CBN domin kai kudi, akwai bukatar ka ziyarci shafin yanar gizo na bankin domin cike form na saka kudin, domin ka samu reference number da zaka yi amfani da ita. (Wanda ya kasa yin wannan, za a bashi form din ya cike a can)
  5. Wanna aiki za a gudanar da shi daga nan zuwa 17 February (wato 17 ga wannan wata da muke ciki) kuma zai a rufe daga wannan lokaci.

Sannan Kuma akwai bukatar bayar da code da Acc da za saka kudin tare da shaidar Dan kasa ko wata shida da aka yarda da ita a kasa. Katin Dan kasa dss tare da lambar nan ta BVN.

Sponsored Links

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button