Advertisment
Education

Anfara Saida form na makarantar collage of health babura dake jahar jigawa.

Sponsored Links

Anfara Saida form na makarantar collage of health babura dake jahar jigawa.

Makarantar collage of health dake garin babura cikin jahar jigawa ta fidda sanarwa Fara sayar da form ga sababin dalibai dake da sha’awar karatun lafiya.

Wannan makarantar dake jahar jigawa cikin karamar hukumar babubar sabuwar makaranta ce Wanda gwabna badaru ya kaita garin na babura inda Nan ne mahaifarsa, wannan shine karon farko da zasu Fara diban dalibai masu sha’awar karatun lafiya a cikin wannan makaranta dake jahar jigawa domin kawo cigaba ga samun ma’aikatan lafiya a cikin wannan jahar ta jigawa dama sauran sassan jahohin Nigeriya.

Hukumar kula da admission da jarabawar dalibai ta makarantar lafia dake garin babura ta fidda sanarwa inda take sanarwa dalibai masu son Shiga wannan makaranta dasu hanzarta su sayi form cikin lokacin da aka ware, Wanda ya kasance daga 09/05/2022 zuwa 22/05/2022.

Ga dukkan masu sha’awar wannan makaranta Ana bukatar dasu ziyarci shafin makaranta Wanda yake kamar haka:-

http://www.consbabura.edu.ng

Bayan sun Shiga Sai a Danna sashen admission a kirkiri account Wanda za’a Yi amfani da cikkyakyan suna, Gmail, phone number, username da password.

Abubuwan da zaku nema Wajen cikewa wato Requirements sun hada kamar haka:-
Ga dukkan dalibin da yake son cikawa dole ne ya mallaki daya daga cikin takadar shedar Gama secondary wato waec, ko neco, sannan dole ya kasance Yana da credit biyar 5 Kuma dole kada ya wuce Zama biyu 2 na jarabawar Gama karatun secondary dayayi.
Ya kasance ya mallaki credit 5 a cikin courses Wanda ya hada da English, mathematics, Physics, chemistry da biology.

Ka shedi:- Ga masu amfani da certificate na Jarabawar Nabteb kada su hadata da kowanne certificate, ma’ana bazasu hadata da waec ko neco ba dole ne ya kasance da ita kawai zasuyi amfani sannan dole ne ya kasance suna da credit 5 a courses din da aka ambata na English, mathematics, Physics, chemistry da biology.

Ku sani wannan from zai kasance a bude tsawon sati 2 wato daga 09/May/2022 har Zuwa ga ranar 22/May/2022.

Zaku iya aika korafi yayin da bukatar hakan ta taso ta hanyar aikawa da sako ta wannan Gmail address din dake kasa

Info@consbabura.edu.ng
Ko Kuma ku Kira daya daga cikin number wayar dake kasa.

08039396223, 08036825516.
Lokacin Kiran dole ne ya kasance daga Monday zuwa Friday sannan a tsakanin lokuta 8 na safe zuwa 4 na yamma.
Amma zaku iya aika sako ta WhatsApp a kowanne lokaci.

Allah ya bada nasara.

Ziyarci shafukanmu na:
WhatsApp group1

Facebook page

WhatsApp group 2

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button