Shugaban kungiyar mallaman Jami’o’in nigeria Asuu farfesa victor Emmanuel osodeke yace Nan ba dadewa ba zasu koma bakin aikin koyarwar da suke Yi
Ya bayyana hakan ne yayin da ya gana da kakakin majalissar wakilan nigeria, femi Gbajabiamila a ranar litinin
Farfesa osodeke ya yabawa matakin da majalissar wakilan kasar ta dauka na tsoma Baki domin anyi sulhu tsakanin gwamnatin da kuma kungiyar mallaman Jami’o’in wato Asuu
Wacce ta kwashe wata takwas tana yajin aikin
Wani bidiyo da aka wallafa a shafin tuwita na majalissar wakilan nigeria ya nuna farfesa osodeke Yana cewa sun kusa kawo karshen yajin aikin
Wanda zuwa yanzu dai tuni labarin saura kiriss asuu ta janye yajin aiki ya watsu a kafafan yada labarai sosai
Ana sa ran dai asuu zata janye yajin aikin da ta Dade tanayi Nan da kwana biyu
Also Read: An Fara Gudanar Da Physical Screening Na Nigerian Customs