Advertisment
Education

Kungiyar malaman Polytechnic Wato ASUP Sun Janye yajin Aikin Gargadin Da Suka Shiga.

Sponsored Links

Kungiyar gamayyar makarantu ta polytechnic wato ASUP ta janye yajin aikin data shiga…
Wannan kungiya me suna academic staff Union of polytechnic ta janye yajin aikin gargadi data shiga na tsawon mako biyu 2 weeks inda ta umarci dukkan dalibai tare da malamai dasu hanzarta komawa makarantu domin cigaba da karatu da ayyukan makarantu.

Kamar yadda wannan kungiya ta sanar dacewa lokacin data dauka na yajin aikin gargadi ya Kare domin haka gobe litinin 30 ga wata za’a cigaba da karatu da sauran ayyukan makarantu.

Chairman na kungiyar ta ASUP yace suna fatan yajin aikin gargadi da suka gudanar ya saka Gwabnatin tarayya ta dubi bukatunsu Wanda sune suka tursasa su suka Shiga wannan yajin aikin.
Shugaban na kungiyar ta ASUP yace akwai abubuwa guda biyar 5 da suke bukatar Gwabnatin tarayya ta biya musu sannan akwai adadin kudi kimanin N15Bn da suke biyan Gwabnatin tarayya ta Nigeriya.
Ya Kara da cewa wannan alkawari ne Wanda shugaban federal ministry of finance da minister of education ya daukar musu akan zasu duba bukatunsu.

Shugaban na kungiyar ta ASUP yace yanxu haka suna kokarin gudanar da zabukan shugabanin makarantu na federal polytechnic mubi da kaduna da sauransu.

KunMuna fatan kungiyar ASUU ta University zasu bi sahun ASUP Suma su koma makaranta duk da a halin yanxu sun haura kwana 100 suna yajin aiki Kuma Babu wani bayani akan zasu koma.!

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button