Sabuwar Sanarwa Daga Hukumar Hukumar Nasims ta Npower da Masu Cin Gajiyar Npower Batch C Stream 2.
Hukumar ta Nasims ta sake fidda sabuwar sanarwa a yau ga dukkan sababin ma’aikatan da za’a dauka acikin wannan batch C stream 2.
Wannan sanarwa tana ga masu zuwa physical screening Wanda aka Fara shi a wannan ranar ta talata saide Kuma ayau din an samu sabuwar sanarwa.
Sanarwar itace ga dukkan masu Degree, Diploma da NCE zasu je ofishin sakateriya dake karamar hukumar su wato local government domin a tantance su ayi musu physical screening.
Ga Wanda Suka Shiga da Secondary school certificate ko Kuma Wanda Basu da certificate ma’ana Wanda basuyi karatu ba dukkansu zasuje center inda aka turasu ma’ana Wajen da zasu karbi training/horo na aikin Npower anan to za’a tantance su.
Allah y taimaka
Also Read: Hukumar Kula Da Npower Batch C Stream ii Sunsaka Ranar Da Za’a Fara Physical Screening