Sabuwar Sanarwar Ga Wanda Suka Cika Karbar Horo Da Gasa Na Cyber Security
Ma’aikatar matasa da cigaba wassanin ta kasa (FMYSD) tare da hadin gwiwar kungiyar Halogen sun Fara tura sakon gayyatar Wadanda sukayi nasarar samun horo da tsaro na FMYSD/HG Cyber security kyauta
Ku tuna cewa Ma’aikatar tare da hadin gwiwar kungiyar Halogen sun kaddamar da horo kan tsaro yanar gizo kyauta
Wanda akalla zasu bayar da horo a yanzu ga matasa mutum 40k Kan dabarun tsaro na internet Wanda zai bada damar rage hadurran Kai hare-hare ta internet, tare da wasu shirye shiryen bayar da tsaro ga Harkokin internet
Wanda tuni wasu har sun Fara karban horon su ma a jiya laraba ranar 31/August/2022
Ga Wanda suka naimi aiki zasu iya duba mail din su domin ganin nasu sakon ko an turo musu
FMYSD/HG zasu bayar da horo kan tsaro harkan yanar gizo
Zaka Sami takardar shaidar samin horo akan cyber security
Kungiyar ta bayyana cewa da wannan certificate din mutum zai iya samun aiki a gida nigeria ko kasashen waje
Sannan kuma kungiyar zata bayar da kyautar kudade ga Wanda suka Sami Nasarar kammalawa daga na daya zuwa na uku
Na farko zai Sami kyautar naira miliyan daya 1million
Na biyu zai Sami kyautar naira dubu dari shida da hamsim 650k
Na uku Kuma zai Sami kyautar naira dubu dari uku da hamsim 350k
Fatan alkhairi Yan uwa
Also Read: Sabuwar Labarin Yajin Aikin ASUU