Rundunar tsaro ta sojojin ruwa (NIGERIA NAVY) zasu bude Portal nasu domin Daukar Sabbin Ma’aikata
Bude portal din zai kasance ranar lahadi 7/08/2022 sannan zasu rufe ranar 17/09/2022
Ga masu sha’awar cika wannan aikin sai ku tabbatar kun zauna cikin Shiri
ABINDA YA KAMATA KA SANI AKAN CIKA AIKIN
Babbar matsala da muke samu yanzu shine yawanci muna samin matsala a shekaru ko wasu Abubuwan namu da munsan tsakanin wata takarda tamu da wata takarda tamu akwai banbanci wani Abu
To Yana da kyau duk Mai Sha’awar cika wannan aikin da ya Sami takardunsa ya daidaita komai nasa daga Kan suna har shekaru
Samin banbanci wani Abu yakan hanamu samin approve a dukkan wasu Abubuwa da Muka cika
Ku kasance damu da zarar an bude shafin zamu sanar da ku
Allah ya bada sa’a