Advertisment
notice

Tayaya zamu Gane Fake alert? Akwai yiwuwar zai yawaita a wannnan tsarin na cashless policy da ake ciki yanxu.

Sponsored Links

Tayaya zamu Gane Fake alert? Akwai yiwuwar zai yawaita a wannnan tsarin na cashless policy da ake ciki yanxu!

Wannan tsarin da akeso a tabbatar dashi a wannan kasar tamu na Cashless Policy zaizo da abubuwa da dama musamman Cyber Crime irinsu Fake Alert, kutsen asusun banki makamantansu, dan haka dole mu koyi sanin yadda zamu gane wadannan abubuwan domin kare kawunan mu da fadawa hannun macuta kuma yan damfara, tun kafin Nigeria tashiga wannan tsarin na Cashless andade anayin Fake Alert kuma an daɗe ana cutar mutanen mu yan kasuwa da wannan tsarin musamman masu POS.

Akwai hanyoyi guda biyu da suke bi wurin yin wannan Fake Alert, hanya ta farko mai sauki ce wurin yi kuma mai sauki ce wurin ganewa, hanya ta biyu itace mai wahala wurin yi kuma mai wahalar ganewa, hanya ta farko suna amfani da kusancin dake tsakaninka dasu ko kuma samun damar karbar wayarka suyi saving Number wayarsu a cikin wayarka da sunan bankin da kake amfani dashi.

Misali: Zasu karbi wayarka sai suyi Saving Number su da sunan bankin da kake amfani dashi kamar First Bank haka bayan wani lokaci sai su shiga cikin wayarsu su nemo ainahin Credit Alert da banki suka taba tura masu sai su shiga suyi Copy nasa, suyi Editing su cire Time na Message din su sanya daidai lokacin da zasu turo maka Message da sauran abinda yakamata su cire sai su tura maka.

Kai kuma yana zuwa batareda ka duba Balance ba, da zaran kaga sunan bankinka tareda rubutun Alert sai kawai kayi tunanin dagaske Real Alert ne.

Hanya ta biyu akwai Website da Application da ake amfani dasu wurin yin Fake Alert amma wannan hanyar ta wadanda suka dauki abun sana’a ne wato waɗanda sukeyin abun dagaske, kuma irin wadannan hanyoyin sai ma kabiya kudi sannan zasu baka damar kayi amfani da ita yin Fake Alert din, acikin Application din akwai “Cardro Pro v8.5” da kuma websites kala- kala da akeyin Bulks Message, ta amfani da wannan Application din idan zasu turo maka sakon Alert bazasu turo da Complete sunan banki ba, kamar idan zasu saka Sterling Bank sai sun saka Starling bank kaga Instead of su saka “E” sai suka saka “A” ko kuma idan First Bank ne sai su saka First bank, a maimakon su saka letter “S” sai su saka dollar sign ($) ko UBA kuma sai su saka VBA, a maimakon “U” sai su saka “V” idan baka lura ba a haka zaka gani sai kayi tunanin Real Alert ne tunda daman ka riga da kasan cewa Bank idan suka turo maka da Alert yana zuwa batareda baka damar kayi Reply ba to suma ta amfani da irin wadannan Applications din Alert zaizo batareda baka damar kayi Reply ba.

Note: Irin wadannan Applications din babu su a Playstore saboda Playstore baya ajiye Applications da zasuyi Harming mutane, dan haka sanin sunanta bazai baka damar ka iya gano inda zaka sameta ba.

Taya Zan Gane Alert Din Karya…?

Abun na farko dan’uwa Idan banki suka turo Messages ba’a masu Reply. Zakaga a wurin reply din sun rubuta “Sender Doest Not Support Replies”. Abu na biyu ka duba sunan Bankin daga cen sama ka tabbatar sunan ba Mistake a jiki, abu na ukku Idan kaga Alert din yazo daban a maimakon yazo tareda sauran Alert din da kake dasu a akwatin message dinka ya jeru dasu bawai ya ware kanshi ba. Misali idan ka duba Alert din da bankinka sukeyi maka duka Alert din suna zuwa ne a Box daya, wato a layi daya babu wani Message da suke jeruwa dashi, to shi Fake Alert ware kanshi yakeyi daban.

Babbar hanyar gane Fake Alert shine idan bakaga Alerts message din a cikin jerin Alert din da kake recieving ba da kuma ya kasance kana Checking Balance domin tabbatarwa.

Allah ya kare mu daga sharrin su.

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button