Advertisment
General

Yadda Zaka Duba sakon karban bashin Nyif idan baka ga sako daga banki ba.

Sponsored Links

Yadda zaka duba kaga kudin Nyif idan baka ga sakon alert daga banki ba.

Wannnan ya kasance abunda yake ta damun dubannin mutane yayinda wasu sukace sunga sakon karban bashi Wanda Nyif ta sahale musu Amma wasu Basu gani ba duk da cewa suna cikin mutane dubu goma da sukayi horo sannan sun bude asusun banki na NPF yayin da akace su bude.
Idan hakan ta faru da Kai ga hanyoyi guda biyu masu sauki Wanda nasan zaku iya binsu kuyi ba tare da kaje cafe ko kaje banki ba domin dubawa ko kaima an turo maka kudin bashin na Nyif.

HANYOYIN BIYU SUNE KAMAR HAKA:-
Da farko ga masu amfani da smart phone Android ko iPhone zaku iya zuwa play store ga masu Android ko appstore ga masu iPhone kuyi download na manhajar NPF bank zasu bukaci kuyi register wacce babu wahala full name ne Sai BVN Sai number asusun ta NPF Sai ka kirkiri password naka dasauransu,
Kuna gamawa zaku ga adadin kudaden dake cikin asusun na bankin wato idan an turo ma zaka gani. Kamar yadda zaku gani ga photo a kasa.

manhajar NPF banki


Na biyu ga Wanda Basu da Android ko iPhone abu mafi muhimmanci da zasuyi shine su tura kudi cikin NPF banki nasu, misali zasu iya tura naira 100 ko kasa da haka da sauransu. Anan zaku gani idan har an turo kudi to zaku gani a balance. Kamar yadda zaku gani a photo dake kasa


To wannan shine yadda zaku bi domin dubawa ko kunyi nasarar samun wannan bashin na Nyif.

Shiga WhatsApp group namu
👇👇👇👇

WHATSAPP GROUP 2 WHATSAPP GROUP 1 FACEBOOK PAGE

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button