Advertisment
Tech & Guide

Yadda Zaka Gano Barawon Waya A Duk Inda Yake (Mobile Tracker Free)

Sponsored Links

Barka da zuwa shafinmu a wannan lokaci Insha Allahu zamu nuna maka wata hanya wanda idan an sace maka wayarka zaka iya ganin wanda ya dauke ta cikin sauki kai harma idan ya dauki Hoto da ita ko kuma yayi kira da ita duk zakaga wannan abu kuma zakaji abinda yace.

Mobile Tracker Free:

Mobile tracker free wani sabon application ne wanda ake dorashi akan wayar hannu wanda zai baka dama karinga ganin duk abinda wayar take dauke dashi ko kuma akeyi da ita.

Abubuwan da wannan application din yake iyayi:

SMS/MMS: zakaga sakon da aka turo ko kuma aka tura da wayar.
Calls: zakaga dukkanin kiran da akayi ta wayar.

GPS Locations: zaka iya ganin location na wayar.
Photos/Images: zakaga duk hotunan dake wayar ko da an gogesu.
Social Networks: zakaga duk sakunan ka na WhatsApp, Facebook da daisauransu.
Yadda Zakayi Rijista:

Da farko zaka shiga wannan link din: https://mobile-tracker-free.com/bayanka shiga daga sama zakaga inda akasa Register to saika danna domin yin rijistar.

Bayan kammala rijistar to akasan page din download daka danna zai fara dazarar ya kammala saika danna install shikenan. Idan kuma duk baka gane wannan bayani ba zaka iya shiga wannan link din domin ganin yadda abun yake https://mobile-tracker-free.com/help/.

Ta ina zan dinga ganin komai na wayar nawa?

Dama tun a wajen rijista akwai Username da kuma Password wanda da shine zaka iya shiga https://mobile-tracker-free.com/login/.

Wannan app yana da matukar mahimmanci musamman a wannan lokaci da ake sace sacen wayoyin hannu dayayi yawa domin taimakawa yan uwa da abokan arziki taimaka kayi Share domin al’umma su amfana.

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button