Advertisment
Tech & GuideUncategorized

Yadda Zaku Tura Kudi Zuwa kasashen Waje ko Cikin kasar dakuke koda baku da bank ko ATM.

Advertisment

Yadda zaka tura kudi zuwa Nigeria ko kuma wasu kasashen Koda baka da bank ko ATM.

Yadda zaku tura kudi zuwa Nigeria ko kuma wasu kasashen Koda baka da asusun banki ko Kuma ATM cikin Sauki.

Munyi tunanin kawo wannan Shirin domin sanarwa Wanda Basu sani ba, Koda Wata Rana bukatar hakan zata taso.

Zaku iya turo kudi ko Kuma ku tura ga kasashen da kuke son turawa misali kasashe kamar Libya, Gabon, Niger, Cameron, Ghana Gambia da sauran kasashe na duniya.

Kamar yadda kuka sani kudin wasu kasashen yafi na Nigeria daraja, to misali kana son turawa wani Dan uwanka ko abokinka kudin Wata kasar Wanda yafi na Nigeria daraja sannan kana son wannan kudi ya Isa hannunsa ba tare da ansaja shi zuwa naira ba to zaka nemi Western Union bank mafi kusa dakai.
Shi Western Union asusun banki ne Wanda aka Samar dashi domin tura kudade daga wannan kasar zuwa Wata kasar ta dukkan fadin duniya, wannan banki na Western Union yafi shekaru ashiri Yana aiki sannan ahalin yanxu akwai shi a kusan dukkan kasashen na duniya.

Nasan zaku iya sanin wannan banki na Western Union ta hanyar ganin allon hotonsa na talla ko Kuma wani Abu daban, Amma zamu iya cewa akwai mutane da Basu San amfaninsa ba Wanda shine tura kudi daga wannan kasar zuwa Wata.
Idan baka taba sanin wannna banki ba ko Kuma baka San inda zaka same shi ba a inda kake rayuwa to hanya mafi sauki idan kana amfani da wayar Android zaka iya search/dubawa ta Google maps ka gano inda yake cikin sauki sannan ka gano mafi kusa dakai domin suna da rassa bila adadin a fadin kowacce kasa.

Da farko zaku shiga opera Wanda kuke amfani da ita ku shiga Google kuyi search kamar haka (Western Union agent finder) Yana budewa zaku ga jerin bayanai sun fito, to Sai a shiga na farko zai nuno find location inda zaku ga Wajen da zaku saka sunan kasar da kake Neman wannan bankin na Western Union da Kuma garin da kake.

Misali kana zaune a kasar Gabon to awajen kasa saiku saka (Gabon) sannna awajen da zaku saka sunan gari wato address saiku saka libreville daga can kasa zaku ga continue anan zai Nuno muku jerin sunaye da Wajen da suke da Kuma number su ta bankin na Western Union saiku zabi na kusa daku domin kuje ku tura kudinku.

ku kalli yadda zaku Yi search na address din Western Union a Google idan Kuna bukatar samosu, saide karku manta munyi amfani da kasar Gabon ne saboda misali Amma Kai idan zakayi ta yiwu a Wata kasar kake daban to address din kasar da garin da kake zakayi search mungode.

Zaku zabi na farko ne

Daga Nan zai Nuno muku Nan

Anan zaku zabi kasar da Kuma garin da kuke Neman address na Western Union bank

Daga Nan saiku shiga continue inda zai nuna muku address na Western Union dake wannan garin da kuke nema saiku zabi mafi kusa da ku.

Anan zaku ga Wajen da zaku samu Western Union Bank saiku zabi mafi kusa da ku.

Saide wasu Western Union din Ana samunsu a cikin wasu bankinne misali zaku iya ganin kamar union bank ko Eco bank suna da Western Union a cikinsa.

Saide Kuma su Western Union suna tura kudi ne ta hanyoyi guda biyu,

  1. Ta hanyar tura kudi zuwa asusun banki na Wanda zai karbi kudin.
  2. Ta hanyar bashi tsabar kudin a hannunsa.
    Amma ya kamata ku sani dukkan Hanyoyin biyu na tura kudi ana biyansu kudin aikawa saide turawa ta bankin me karba yafi rangwame akan turawa ta tsabar kudi.

Akwai mataki biyu ga Wanda yake so a turawa Wanda zai karbi kudin hannu da hannu.
Na farko: Da zarar ya Isa wannan bankin zai sanar dasu Yana son tura kudi kuma wand zai karba Yana so ya karba hannu da hannu, to zasu bashi form ya cike anan zai saka sunansa da sunan Wanda za’a turawa, address nasa, adadin kudaden da za’a tura da sauran bayanai..
Na BIYU:- akwai wani resiti da code da zasu baka me suna MTCN Kai Kuma zaka turawa Wanda zai karbi wannan kudi wadannan lambobi na MTCN Wanda Yana zuwa Western Union na kasar da yake idan ya Basu zasu bashi wannan kudi anan take.

Ga masu turawa ta bankin Wanda zai karbi kudin hannu da hannu,
Shikuma Bayan yaje Western union sun bashi form ya cike zai saka sunansa da sunan me karba da bayanan bankinsa.
Saide shi resiti zasu bashi Banda lambobi na MTCN saboda shi ta bankin za’a turawa Wanda zai karbi kudin ba ruwansa da zuwa bankin Western Union saide suga sako daga banki su.

Ya kamata ku sani turawa Wanda zai karbi kudin ta cikin bankinsa yafi sauki da Kuma rangwamen kudin da za’a karba wato charges fees akan Wanda za’a turawa ya karba hannu da hannu.

Da fatan Kun amfana da wannan post namu Muna muku fatan nasara!

Ziyarci shafukanmu na:-

WhatsApp group 1

Facebook page

WhatsApp group 2

Ziyarchi Shafukanmu Na WhatsApp group 1, WhatsApp group 2, WhatsApp group 3, Facebook page, da Telegram.

Advertisement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Advertisment

Join our WhatsApp group for more information


<
Back to top button