Yadda Zaka Gane Sakon Approve Na Gaskiya
Assalamu alaikum
Yau muna tafe da yadda zaka Gane sakon approve na gaskiya
Zuwa yanzu Haka an Sami Bata gari masu son suga sun cuci Al’umma suna ta faman turawa mutane da fake sako na kancewa anyi approve nasu
Wasu suna tura hakan ne da manufar kayi musu reply su ce sai ka biya wasu kudade sannan zasu turo maka da kudin
Wasu Kuma suna yin Haka ne da manufar su Sanya maka link na website a kasan sako ka Shiga su karu da Kai wasu Kuma suna yin hakan ne da manufar su Sami details naka ko na bank account naka domin su debe maka kudin account din ka ko idan Babu su ciyo maka bashi Wanda Kuma Dole sai ka biya
A saboda Haka ne muka ya dace mu sake sanar da ku domin mu sake tsiratar da Kan mu daga Sharrin masu son cin amanar mu ko su cuce mu
A duk lokacin da kaga an maka sakon approve indai baiyi dai dai da irin wannan sakon kasan ba kada ka yarda da shi
Sannan a duk lokacin da kaga sako irin wannan na kasan kada ma ka bashi mahimmanci sako ne na Yan damfara
Sannan duk wani sako da zakaga ance maka ka Kira Mrs (wane) kada ma ka Kira Yan damfara ne
Ko kaga sako an turo maka da shi an saka maka link Mai bitly kada ka yarda da shi shima ba sakon approve bane
Fatan alkhairi
Allah ya tsare mu gaba daya
Kasance da shafin GinSau domin sanin mahimman bayanai Akan Abubuwa masu mahimmanci
Also Read: Sabuwar Sanarwar Ga Wanda Zasu Naimi Aikin Immigration