Advertisment
notice

Abubuwan biyar daya kamata ku sani dangane da Shirin Npower batch C stream 2.

Sponsored Links

Abubuwan biyar daya kamata ku sani dangane da Shirin Npower batch C stream 2.

Da yawan mutane Wanda suka nemi aikin Npower batch C stream 2 suna mamakin dalilin dayasa har yanxu Gwabnatin tarayya take ta magana akan fidda jerin Wanda Sukayi nasara amadadin suyi magana akan physical verification wato tantancewa ta Ido da Ido ko Kuma deployment wato turawa Wajen aikin na Npower.

Shine mukayi tunanin ya kamata mu sanar daku wadannan Hanyoyin biyar domin KU kauracewa rudani da Kuma labarai marad inganci.

 1. Abu na farko daya kamata ku sani shine haryanxu fidda jerin Wadanda sukayi nasara a Npower batch C stream 2 Ana Nan Ana gudanarwa.
  Shafin sada zumunta na Facebook Dana Twitter karkashin mallakar ma’aikatar ta tarayya gudanarwa da bala’i da cigaban jama’a a ranar asabar data gabata ta sanar da cigaban da fidda sunayen Yan takarkarun a shafinta na www.nasims.gov.ng,
  Kamar yadda muka sani a January na wannan shekaran wasu daga cikin Yan takarun sunga sakon sunyi nasara lokacin da suka duba a shafin na Npower harma sukayi thumb print Wanda a Wannan lokacin shafin sada zumunta na Facebook na Npower sun karyata wanda sukayi nasara duk da cewa sune suka Dora akan website nasu,
  Akwai mabanbanta labarai akan Wanda Sukayi nasara a wanda sukayi nasara inda wasu ke kiransu da batch c steam 2 wasu Kuma da supplementary duk da wannna bashine abun Lura ba inde kayi nasara to kayi nasara muna Taya murna.
  Wasu daga cikin Yan takarkarun sunga sakon sunyi nasara a wancan lokaci wasu Kuma a satin daya gabata wasu Kuma jiya domin hakan muna da tabbacin wannan aikin na Npower suna Nan suna fidda Wanda Sukayi nasara domin hakan inde kasan ka cike sannan ka duba baka samu ma kana dubawa lokaci zuwa lokaci akwai yiwuwar ka samu a Nan gaba.
  Shin tayaya zaka San ko kayi nasara?
  Hanya daya ce dole ne ka kasance kana duba profile dashboard naka na babban shafin Npower Wanda suke gudanar da abubuwan su wato www.nasims.gov.ng,
  Amma ya kamata ku sani idon kunyi nasarar ganin sunanku bashi ke nufin Kun Gama samun aikin Npower ba domin akwai physical screening duk da cewa wannan inde kana da bayanan ka na kome daka cike yayin Neman wannan aikin na Npower to kamar ka tsallake wannan matakin.
 2. Sannan daukar zannen yatsu wato biometric thumb print haryanxu Yana gudana domin haka duk sanda kaga kayi nasara zaka garzaya internet cape dake kusa dakai kayi thumb print,
  Ma’aikata ta Jin Kai da walwala ta dakatar da Yan takarkarun dasuka Yi nasara a watan February har sai sanda ta bada urmanin dasuyi sannan zasuje suyi, saide Kuma duk Wanda Sukayi shikenan hakan baya nuna da sun rasa Shirin na Npower ko Kuma sunyi kuskure.
  A duk sanda kayi thumb print idan ka koma shafin naka na Npower Bayan wani lokacin zakaga ya nuna fingers print captured, to Yana nufin ka wuce wannan matakin saura na gaba,
 3. Haryanxu babu tabbacin ranar da za’a Dena daukar zannen yatsu na biometric thumb print,
  Don haka Babu bukatar ka damu domin duk sanda kaga kayi nasara zaka garzaya kaje internet cape ka gudanar da shi, Abu me muhimmanci shine kaga kayi nasarar tsallake wa matakin farko wato kaga sun nuna maka congratulations.!
 4. Haryanxu Babu tsayyayen ranar da za’a gudanar da physical screening wato tantancewa ta Ido da Ido shi wannan physical screening Yana faruwa a duk Wata local government Secretariat na dukkan kananun hukumar da ake dasu a fadin nigeria Wanda Sukayi nasara suna zuwa wannan Wajen domin tantancewa sannan Ana bukatar wasu muhimman takardu kamar su certificate wanda ka cike inda da degree ka nema ana bukatar NYSC certificate date of birth certificate, local government indigine, BVN detail slip, passport da sauransu.
 5. Na karshe Ana bukatar Wanda ya cike be samu ba daya Yi hakuri Yana dubawa lokaci zuwa lokaci, duba da yadda yanayin kasar yake akwai dubban matasa marasa aiki sannan sunyi karatu dole ne wasu su samu wasu Kuma su rasa duk da cewa haryanxu ana Nan Ana fidda jerin sunaye na Wanda suka cike indan kaga baka samu ba ka dage da addu’a sannan kana dubawa lokaci zuwa lokaci.
  Akwai babban abinda mutane suka manta shine wannan aikin na Npower Ana fitar da shine batch zuwa batch ma’ana ana daukar sunayen ne daki daki domin hakan haryanxu akwai babban sa rai da dama ga dukkan Wanda suka nema Amma Basu samu ba.
  Muna muku fatan nasara
Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button