Hukumar bunkasa fasahar sadarwar zamani ta kasa (NITDA) ta karkashin cibiyar kere-keren na’urorin zamani “National center for Artificial Intelligent & Robotics” (NCAIR), zata bawa Yan kasa horo akan yadda ake kera na’urorin fasahar zamani gaki da yadda ake sarrafa su.
Horon Za’a gudanar da shi rukuni rukuni , na zaman wani fanni na wani shiti na musamman da hukumar ta NITDA ta tsara domin Horar da Yan nigeria mutum miliyan daya
Wannan dama ce ga duk wani Dan nigeria Wanda ya aura shekara 15 a duniya
Sannan Kuma daga Kan Wanda yake karatun secondary School zuwa University kowa zai iya naiman wannan horon
Sai dai bayar da horon da za ayi ba a online bane a cikin birnin tarayya Abuja za’a gudanar da taron bayar da horon
Wadanda suke matsayin Yan boko Wanda suke koyo ko masu Fara koyo zasu shiga link na kasa domin cikawa
Wadanda Kuma suke da ilimin akan harkan zasu Shiga link na kasa domin cikawa
tindaga yanzu Haka an Fara cika wannan damar sannan Kuma a wannan watan Za’a Fara bayar da horon kamar yadda shafin sadarwa na cibiyar kere-kere ta kasa (NCAIR) ya wallafa