Hukumar Npower ta Fidda Sanarwar Gargadi ga Masu Cin Gajiyar Shirin
Hukumar Npower karkashin jagoranci nasims sun fidda sanarwa ga dukkan masu cin gajiyar Shirin Wanda wannan sanarwa gargadi ce ko muce kashedi.
Sanarwa itace hukumar ta nasims ta gargadi dukkan masu cin gajiyar Shirin dasu guji duk wani sako ko post Akan su tura bayanansu na Npower domin a Basu aikin ko a Sanja musu inda aka tura su ko Kuma ayi musu wani taimako na daban sunce irin wanna sako baya fitowa daga hukumar tasu.
Akwai dubban Yan damfara da suke tura sako ta waya ko Kuma suyi post a shafukan sada zumunta akan zasu taimakawa mutane Wanda suke cin gajiyar Npower kamar redeployment ko Sanja wajen aikin da aka turasu ko Kuma ayi musu physical verification da sauransu, hukumar ta Npower tayi gargadi ga jama’a Akan su tabbatar da sun guje irin wannan sakonni domin ba Daga hukumar Npower yake.
Idan har kana da matsala ko wani Abu ya shige maka duhu to je internet cape mafi kusa dakai domin a warware maka matsalar Amma kada ka yarda da duk Wanda zaka samu a shafukanmu sada zumunta domin mafi yawancinsu Yan damfara ne zasu iya Kwacewa bayananka su saka nasu ta yadda su zasu Mori aikin Npower kaikuma su barka da shan wahala.
Muna muku fatan nasara.
Also Read: Nigeria Army Tasaki Shortlisted Na Wanda Sukayi Nasarar Zuwa Matakin Screening