News
Karon Farko Facebook Yayi Asarar Da Tunda Aka Kafa Shi Baitaba Faduwar Da Yayi Ba
Sponsored Links
Katafaren Kamfanin shafin sada zumunta da muhawara wato Facebook ya samu raguwar masu amfani dashi a kullum (DAUs) karon farko a tarihin sa
Cikin shekaru 18 da kafuwar sa.
Ainahin babban Kamfanin Meta network yace yawan masu amfani da shafin a kullum ya ragu zuwa 1.929billion a cikin wata uku zuwa karshen watan December
Idan Kuma aka kwatanta yadda suke Samu a baya
Bayan wata uku da suka wuce Kamfanin Facebook Yana samun mabiya mutum b1.930billions a kullum
Inda hakan ya jawo faduwar Darajar hannun Karin Kamfanin na meta (Facebook) ta ragu da sama da Kashi 20 cikin dari a cinikayyar Yan sa’o’i a kasuwar new York
Faduwar Darajar ta haifar da asarar kusan dala biliyan 200 (£147.5bn)
Hakan Kuma Darajar hannun jari a sauran shafukan sada zumunta da muhawara da suka hada da Twitter da snap da Pinterest, ita ta Fadi sosai a kasuwar.
Shugaban Kamfanin Facebook ya ce cinikin da Kamfanin yakeyi ya ragu saboda masu amfani da shafin musamman matasa sun koma wasu shafukan abokanan gogayyar Facebook din
Kamar su TikTok Twitter Snap da dai sauran su.
Sponsored Links