Advertisment
support

Me Yasa Aka Samu Tsaiko Wajen Kaddamar Da Pi Mainnet, Wato Pi Launching?

Sponsored Links


Mutane da yawa suna ta ‘korafi cewa har yanzu ba’a kaddamar da Pi Network ba, bayan su Pi din sun rubuta a cikin white paper dinsu cewa za ayi launching Pi Network bayan watanni 6 daga kan December 2021 zuwa watanni shidan gaba, zai kasance June ko July 2022, gashi har an wuce da watanni uku ko hudu, wannan ne dalilin da yasa wasu suke ta cewa ana ta jan rai, ana ta ‘dage rana da lokaci bayan lokacin ya cika, Anya ma gaskiya ne kuwa? zan bayyana me ya jawo hakan, in sha Allah.

~ Abu na farko, kullum mukan ce kafin kayi magana akan Pi Network kaje ka fahimci abinda suka fada a White Paper dinsu, musamman White Paper din da suka fitar a December 2021 guda biyu.
~ Clearly a fili a bayyane suka ce launching din Pi, ko Mainnet sai bayan watanni shida, sai suka ce “But it depends on the maturity of the network”. Wannan maganar me suke nufi?
Abinda suke nufi shine launching din Pi yana da alaka da girman Network din, da yadda duniya ta karbe shi, shi Pi, da farashin da Pioneers suka bashi idan suka tashi canza Pi da kaya ko aiki (Services).
Da Kuma batun KYC da migration, wannan from the technical part kenan.

~ Abinda suke nufi idan acikin watanni shida Network din yayi karfi, abinda ake nufi da Network a nan shine Jama’a, kamfanoni, ‘yan kasuwa da kuma karfin Pi Network din a duniya a wajen mutane dai daiku da hukumomi, idan an samu karbuwa da yarda da Pi kafin watanni shidan su cika, toh tabbas za ayi launching Pi, Kuma External connectivity tsakanin Pi da sauran Network zai kasance a Mainnet.
~ Idan kuma ba’a samu haka ba, toh launching din Pi ya danganci zuwa lokacin da aka samu wadannan abubuwan da muka bayyana a sama☝️.

~ Abu na biyu:
Yanzu haka ‘yan kasuwar kasar China da Korea ne kawai suka bayar da kaya da yawan gaske da Pi, Kuma a GCV ko GCP ($314,159) wato (Global Consensus Value) ko (…Price), so far karfin su yana karewa sosai, saboda muna magana dasu ta hannun Mrs. Doris Yen, duk Wanda yayi zurfi a harkar Pi yasan wacece Doris a China.
~ Daga ko Ina a duniya ana zuwa China a saya kaya a wajen Chinese Merchants, Kuma a farashin GCP, sauran kasashen koda akwai Merchants basu da karfin sacrifices kamar na China, cash inflow dinsu ya ragu kwarai da gaske.

~ Amma duk da haka maganar da muka yi da Mrs. Doris ‘dazu da yamma (Yau Lahadi) ta tabbatar da ana kan tattaunawa tsakanin Chinese Merchants wajen ganin an samu mafita a kusa, samun mafitan shine abinda zai jawo Mainnet din kusa, tunda watanni shidan sun wuce.
~ Dan haka muke zaton Core Team su Nicolas watakil zasu fito suyi addressing wannan issues din for the second time, domin Tunatarwa da bayanin present circumstances da suka taimaka wajen delaying Mainnet.

~ Ana bukatan manyan ‘yan kasuwa, yanzu haka China ce kawai da Kore Ta Arewa suka bayar da Yan kasuwa masu yawa, hakan ya taimaka wajen bude PCM, Wanda kasashe 10 suke ciki, yanzu haka, har da kasashen Africa biyu, Amma abun mamaki babu Nigeria da ake ganin uwa ce, saboda me?
~ Saboda ‘yan Nigerian basu shigo ciki da farko ba, kasar Togo tana cikin PCM da Ivory Coast, yanzu ne muka taso domin saka Nigeria a ciki, Kuma alhamdulillah duk wata ka’ida da Pi Core Team suka bamu mun cike ta, su muke jira.
Hakan da za muyi shine babban taimakon da muke bayarwa ga shirin Mainnet, Wanda kafin sa za’a ga abubuwa a zahiri in sha Allah daga wajen mu.

~ Abu na uku:
Akwai factors da yawa wadanda Pi Network suke amfani dashi domin Shirin Mainnet, daga cikin akwai bayanan da muka saka a sama, sai Kuma transactions da ake yi da Pi, farashin da yafi zama highest akan Blockchain din Pi a Enclosed Network (wato yanzu), shine determining factor na farko wajen bayyana global price na Pi a Mainnet.

~ Shiyasa Chinese suka fi kowa promoting $314,159 a matsayin Pi price...

Idan mun fahimci wannan, Pi Core Team suna tattara bayanan yawan Pi din da aka yi transaction dashi a Enclosed Network a kowace kasa ta duniya.
~ Shin ana hada hada da Pi a Nigeria, Pi nawa aka yi amfani dashi a kasar, da sauran kasashe. Yanzu haka maganar da muke da wasu Merchants yana nuna su kansu suna kokarin hakan ne domin aje Mainnet, da kudin su da dukiyar su.

~ So, Pi Network basu Saba wata ka’ida daga cikin ka’idojin Mainnet ko launching da suka saka ba. Sai dai Kaine baka gane ba, ko kuma kabi hayaniyar mawakin Kanon nan da yayi ta cewa “Kun shafe shekara da shekaru wai Kuna Mining har yanzu ba’a yi launching din da kuke ta cewa Zata fashe ba”.
~ Kaga wannan maganar jahilai akan Pi, ba masu ilimi ba.
Wadanda suke biye Dani sun ga irin shirin da muke yi na kawo sauyi a tafiyar Pi, Wanda na tabbata da zamu bayyana kaso kadan na abinda muke yi a kasa wallahil Aziym da yawa zasu karyata mu, amma mun fi so mu bayyana aiki sama da cewa za muyi, kullum za muyi.

~ Amma tsakani da Allah duk yanda kake tunanin Pi ya wuce nan, domin mu muke magana da Alaqa da kasashen wajen da suke cikin tafiyar, wadanda Kai tsaye daga Core Team muke sanin wasu abubuwan.

~ Allah yasa mu dace….

Abdul-Hadi Isah Ibrahim

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button