Rundunar Sojojin Kasa Na Nigeria Sun Saki Shortlist Na Wanda Sukayi Nasarar Zuwa Matakin Gaba
Da yawan mutane da suka nemi aikin Npower batch C stream 2 suna mamakin dalilin da yasa har yanzu Gwamnatin Tarayya take magana akan fidda jerin sunayen wadanda suka yi nasara maimakon su yi magana akan tantancewa ta ido da ido ko kuma turawa wajen aikin na Npower.
Shine mukayi tunanin ya kamata mu sanar daku wadannan hanyoyin biyar domin ku kauracewa rudani da labarai marasa inganci.
Abu na farko daya kamata ku sani shine har yanzu ana ci gaba da fidda jerin wadanda suka yi nasara a Npower batch C stream 2. Shafin sada zumunta na Facebook da Twitter karkashin mallakar Ma’aikatar Tarayya Gudanarwa da Bala’i da Cigaban Jama’a a ranar Asabar ta sanar da cigaban da fidda sunayen yan takarar a shafinta na www.nasims.gov.ng. Kamar yadda muka sani a Janairu na wannan shekarar wasu daga cikin yan takarar sun ga sakon sun yi nasara lokacin da suka duba a shafin na Npower harma suka yi thumb print. A wancan lokacin, shafin sada zumunta na Facebook na Npower sun karyata wadanda suka yi nasara duk da cewa sune suka dora akan website nasu. Akwai mabanbanta labarai akan wadanda suka yi nasara inda wasu ke kiransu da batch C stream 2 wasu kuma da supplementary. Duk da haka, inde ka yi nasara to ka yi nasara muna taya murna. Wasu daga cikin yan takarar sun ga sakon sun yi nasara a wancan lokaci wasu kuma a satin daya gabata wasu kuma jiya. Domin haka muna da tabbacin wannan aikin na Npower suna nan suna fidda wadanda suka yi nasara. Inda kasan ka cike sannan ka duba baka samu ba, kana dubawa lokaci zuwa lokaci akwai yiwuwar ka samu a nan gaba.
Hanya daya ce zaka san ko ka yi nasara shine ka kasance kana duba profile dashboard naka na babban shafin Npower wato www.nasims.gov.ng. Amma ya kamata ku sani idan kun yi nasarar ganin sunanku, ba shine nufin kun gama samun aikin Npower ba. Domin akwai physical screening duk da cewa wannan inde kana da bayananka na kome daka cike yayin neman wannan aikin na Npower, to kamar ka tsallake wannan matakin.
Daukar zannen yatsu wato biometric thumb print har yanzu yana gudana. Domin haka, duk sanda kaga kayi nasara, zaka garzaya internet cafe dake kusa dakai kayi thumb print. Ma’aikata ta Jin Kai da Walwala ta dakatar da yan takarar dasuka yi nasara a watan February har sai sanda ta bada umarnin dasuyi sannan zasuje suyi. Duk wanda suka yi, shikenan hakan baya nuna da sun rasa shirin na Npower ko kuma sun yi kuskure. A duk sanda ka yi thumb print, idan ka koma shafin naka na Npower, bayan wani lokaci zakaga ya nuna fingers print captured. To yana nufin ka wuce wannan matakin saura na gaba.
Har yanzu babu tabbacin ranar da za’a dena daukar zannen yatsu na biometric thumb print. Don haka babu bukatar ka damu domin duk sanda kaga kayi nasara, zaka garzaya ka je internet cafe ka gudanar da shi. Abu me muhimmanci shine kaga kayi nasarar tsallake wa matakin farko wato kaga sun nuna maka congratulations.
Har yanzu babu tsayayyen ranar da za’a gudanar da physical screening wato tantancewa ta ido da ido. Wannan physical screening yana faruwa a duk wata local government secretariat na dukkan kananun hukumar da ake dasu a fadin Nigeria. Wanda suka yi nasara suna zuwa wannan wajen domin tantancewa sannan ana bukatar wasu muhimman takardu kamar su certificate wanda ka cike inda da degree ka nema, ana bukatar NYSC certificate, date of birth certificate, local government indigine, BVN detail slip, passport da sauransu.
Na karshe, ana bukatar wanda ya cike be samu ba daya yi hakuri yana dubawa lokaci zuwa lokaci. Duba da yadda yanayin kasar yake akwai dubban matasa marasa aiki sannan sunyi karatu dole ne wasu su samu wasu kuma su rasa. Duk da haka, har yanzu ana nan ana fidda jerin sunaye na wanda suka cike. Inda kaga baka samu ba, ka dage da addu’a sannan kana dubawa lokaci zuwa lokaci. Akwai babban abinda mutane suka manta shine wannan aikin na Npower ana fitar da shine batch zuwa batch ma’ana ana daukar sunayen ne daki-daki. Domin hakan, har yanzu akwai babban sa rai da dama ga dukkan wanda suka nema amma basu samu ba. Muna muku fatan nasara.
Rundunar sojojin kasa ta nigeria ta bayyana cewa a na’ura Mai kwakwalwa (computer)
Also Read: Aliko Dangote Zai Dauki Ma’aikata Wanda Suka Gama Karatun Digiri a Bangaren Engineering