Advertisment
News

Aliko Dangote zai dauki ma’aikata Wanda suka gama karatun digiri a bangaren engineering.

Sponsored Links

Aliko Dangote ya sanar da daukar ma’aikata Wanda suka gama karatun digiri a bangaren engineering.

Kamar yadda kowa yasani Aliko Dangote shine Wanda yafi kowa kudi a nahiyar afrika sannan bakin fatar daya fi kowanne Baki kudi a duniya, Kuma Yana daga cikin masu kudi na duniya.

Masana’antar sa ta Dangote refinery ta kasance sabuwar masana’antar Wanda Aliko Dangote ya kirkira acikin wadannan shekaru wacce yayiwa Yan kasar Nageriya alkawarin daukar ma’aikata Wanda suka gama karatun digiri a bangaren engineering saide wadannan ma’aikata da za’a dauka zasu kasance sababin dalibai Wanda Basu Dade da Gama karatu ba.

Wannnan babban kamfani ya kudurci aniyar daukar sababin ma’aikata Wanda suka gama karatun digiri sannan suka samu sakamako Mai kyau a makarantar da suka kammala.

Wannan kamfanin na Dangote refinery zai dauki Wanda suka gama karatun su na digiri sannan Wanda Basu haura shekaru 30 da haihuwa ba sannan Wanda suka kammala da sakamako Mai kyau kamar First class ko second class honor.

Kamar yadda kamfanin ya sanar ya turawa makarantar kimiyya da fasaha ta abubakar tafawa balewa cewa su tura musu sunayen dalibai Wanda suka kammala karatun a wannan jami’ar ta abubakar tafawa balewa a shekarar daga 2019, da shekarar 2020 dakuma shekara ta 2021 domin su tantance su sannan su zabi Wanda suka cancanta.

Wannan kamfani ya Kuma ware bangaren daya kamata dalibai su nemi wannna aikin Wanda ya hada da:-
chemical engineering, mechanical, electrical, and electrical/electronics engineering, da sauransu sannan dole su kasance Wanda Sukayi karatu acikin wannan kasa Mai albarka wato Nigeriya.

Ku kasance damu domin Jin lokacin da za’a Fara daukar wannan aikin.

Allah ya bada nasara.

Ziyarci shafinmu na:-

WhatsApp group 1

Facebook page

WhatsApp group 2

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button