Yadda Zaka Gyara Matsalan Rufe Layi Da Kamfanin Sim Card sukeyi

Kamar yadda kowa ya sani company sim card sun rufewa mutane layukan su na waya sosai
Saboda rashin hada sim din su da Nin number
Wasu Kuma sun hada Amma hakan ma Bai Hana sun kulle musu sim card nasu ba
Idan har kana cikin wadanda Suka rufewa sim kuma har yanzu Basu bude maka ba
To ga dalili da yasa suka rufe maka shi
Rashin yiwa layi register da sunan da yake Kan nin number naka
Misali nin number Dinka
Musa
Sunan da kayi register Layin ka da shi Ibrahim
To baza su karbi nin din Nan ba
Matsalan na’ura daga hukumar hada nin da layuka
Rashin kammala register
Matsalar yanar gizo
Kuskure wajen shigar da number nin
Wadannan suna daga cikin Abubuwan da yasa suka rufe maka sim baka
Amma insha Allahu ga hanyar da zakabi ka gyara sim card naka yadawo aiki
Abin da yakamata kayi shine
Idan har ka tabbatar da ka hade sim din ka da nin number Amma kuma duk da hakan Layin baya Kira to ka Garzaya ofishin sadarwa na Layin da kake amfani da shi
Ka fada musu matsalar ka
Kamfanin sadarwa basuji dadin kaste layukan customers nasu da sukayi ba
Saboda sun tabka asarar kudin shiga Mai yawa ta dalilin rufewa mutane layukan su
Amma idan harka shigar da korafi zasuyi saurin bibiyar ka domin su Bude maka da sim card din ka ya dawo aiki
Fatan nasara