Advertisment
Job

Yadda zaka cike aikin sojan Sama wato air Force da danka

Sponsored Links

Babbar sanarwa ga Wadanda suka cika aikin air Force.
Dole ne ga dukkan Wanda yake son Neman aikin air Force ya tanadi wadannan abubuwan kamar haka:-
Na farko: Dan takarar Neman aikin dole ne ya kasance Dan kasar Nigeria Kuma ya mallaki katin Dan kasar.
Na biyu: shekarun sa dole ne ya kasance akalla daga 18 zuwa 22.
Zai Zama dole an haifeshi kafin 31 ga watan March na shekarar 2022.
Na uku:- dole ne me cikawa ya kasance marad aure,
Na uku:- dole ne tsayin sa ya kasance kamar haka, ga maza 1.66 fadin kirgi da 5.4 tsayi. Ga Mata 1.63 fadin kirgi da 5.3 tsayi.
Na hudu:- dole ne ya kasance Yana da takardar shedar lafiya.
Na biyar:- dole ne ya kasance Yana da takardar shedar Zama Dan karamar hukuma wato local government, sannan dole ya samu saka hannu na jami’in soja Wanda dole ne kada ya kasance yayi kasa da matsayin wing commander na jami’in sojan Sama.
Na shida:- dole ne ya kasance ya gabatar da takadar su na karatu masu inganci tare da kananun hoto wato pass port, sannan da ingantattun takardu kamar haka:-
A. Takardar shedar haihuwa.
B. Takardar shedar Gama karatu wato na secondary.
C. takardar shedar Zama Dan karamar hukuma wato local government indigenes.
D. Takadar shedar wani jami’in sojan Sama..

Sannan Bayan angama cikewa wanann form na aikin soja dole ne ya kasance Kuna da abubuwan kamar haka:-
A. Takardar shedar Gama cikawa wato acknowledgement slip.
B. Takardar saka hannun wani jami’in sojan Sama.
C. Takadar shedar Zama Dan karamar hukuma wato local government indigine.

Ga dukkan Wanda suka Yi nasarar samu fito a list dazai fito za’a gayyace su zuwa tantancewa.
Ga Wadanda suka nemi bangaren Non-tradesmen/women dole ne ya kasance suna da credit biyar a waec neco ko napteb, Wanda ya hada English, mathematics a zaman zana jarabawar da be haura biyu ba.

Ga Wadanda suka cika drivers da trade skills dole ne su mallaki waec, neco ko napteb. Sannan su samu credit a English a cikin certificate nasu.
Haka zalika ga Wanda suka cika bangaren sportsman/women dole ne su bayyana certificate na kwarewar su a wannan fanin.

Abin Lura:- babbar sanarwa ga dukkan Wanda suke da HND ko Degree bazasu cike wannan aikin na sojan Sama ba. Sannan dole ne masu cikawa su karanta muhimman dokokin aikin sojan Sama kafin su cika.

danna shudin rubutun dake kasa domin cikawa

APPLY NOW

shiga WhatsApp group namu

whatsapp group

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button