News
Related Articles
Check Also
Close
-
Anfara Tura Sakon Karban Bada Bashin GEEP 2.0April 8, 2022
Za a gudanar da sabon kidayar jama’ar Najeriya bayan shekaru 15 da yin kidayar karshe. Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa, Nasir Isah Kwara, ya bayyana cewa za a yi amfani da fasahar zamani wajen aiwatar da sahihiyar kidayar da kuma karbabbiya wajen al’umma. Ana sa ran gudanar da kidayar ne a watan Mayu na wannan shekarar.
A baya, wasu daga cikin jihohin kudu ba su yarda da sakamakon kidayar da aka yi a shekarar 2006 ba, inda suka zargi an yi musu magudi domin a fifita yankin arewa. Kiyasin ya nuna cewa al’ummar Najeriya sun kai miliyan 200, inda aka kwatanta miliyan 140 da aka samu a 2006. Sai dai zuwa yanzu ana kiran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da takamammiyar ranar da za a yi kidayar.
Also Read: Shugaban KAROTA na Jihar Kano Ya Yi Kalamai Masu Zafi Kan ‘Yan Adaidaita Sahu