Advertisment
News

Shugaban KAROTA na Jihar Kano Ya Yi Kalamai Masu Zafi Kan ‘Yan Adaidaita Sahu

Sponsored Links

Shugaban hukumar KAROTA na Jihar Kano, Baffa Babba Dan Agundi, yayi kalamai masu zafi akan ‘yan adaidaita sahun Kano.

‘Yan adaidaita sahu a Kano sun shiga yajin aiki ne ranar 10 ga watan Janairu na 2022.

Gidan Radio Freedom sun yi hira da shugaban hukumar KAROTA na Jihar Kano, inda yayi wa ‘yan adaidaita sahu martani da cewa lallai matukan adaidaita sahu zasu gane shayi ruwa ne. Ya ci gaba da cewa wannan yajin aikin da suka shiga kilce zai jawo musu ba daɗi.

Ya kara da cewa shiga yajin aikin ba zai haifar musu da mai ido ba, domin kuwa yace zai kawo musu wasu sabbin abubuwa. Sannan ya kara da cewa, yanzu haka rashin ‘yan Napep a Kano yasa ana tuki mai tsafta ana bin dokokin tuki.

Also Read: Za a Yi Kidayar Jama’ar Najeriya Bayan Shekaru 15

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button