Advertisment
News

SUBHANALLAH:-Wani Dalibi Yayiwa Abokinsa Yankan Rago A Makaranta Secondary Dinsu

Sponsored Links
KIRA ZUWA GA MAIGIRMA GWAMNAN JIHAR BORNO
wannan Abu ya faru ne a jihar Mai duguri cikin  makarantar El kanemi college of Islamic theology Mai duguri 
sunan dalibin Jibrin Sadi Mato
An samu wani Dalibin makarantar babban azzalumi Senior na Jibrin Sadi Mato ya masa yankan rago saboda wani ‘dan sabani da ya shiga tsakaninsu a makaranta
Yanzu haka Jibrin yana kwance a sashin bada agajin gaggawa na Asibitin koyarwa dake Maiduguri Intensive Care Unit (ICU)
Likitoci suna kokarin ceto rayuwarsa da take dab da salwanta
 Amma babban abin bakin ciki shine, shugaban makarantar El-
Kanemi College of Islamic Theology Maiduguri suna kokarin
rufe maganar, saboda wanda ya aikata ta’addancin dan gidan wani babban mutum ne a Maiduguri
Mahaifin Jibrin ya bukaci a sanar da duniya halin da ake ciki
domin a musu adalci, da wannan muke kira ga Maigirma
Gwamnan jihar Borno Professor Babagana Umara Zulum ya
san abinda yake faruwa tare da daukar matakin gaggawa akan shugaban makarantar
Muna rokon jama’a su taimaka wajen yada wannan sakon ya isa duk inda ya dace
Muna rokon Allah Ya bawa Jibrin lafiya, Allah Ya tona asirin wanda ya masa yankan rago
fitatcen marubucin Nan na kafar sadarwa na Facebook wato datti assalafi ne ya wallafa wannan rubutun a safiyar yau juma a 21january2022
muna rokon Allah ya kawo Mana karshen wannan masifu da suke addabar mu
Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button