Advertisment
News

An Kama masuyiwa Yan fashin daji safarar karuwai

Sponsored Links
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama mutum 26 da take zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da mata huɗu da ake zargi suna aiki tare da wani gawurtaccen ɗan fashin daji a Jihar Kaduna.
Da yake gabatar da waɗanda ake zargin a ofishin rundunar gaggawa ta IRT ranar Talata, kakakin rundunar ta ƙasa Frank Mba ya ce matan da kuma wani namiji sunayi wa ‘yan fashin daji safarar karuwai zuwa cikin daji.
Ya bayyana sunayen matan sune kamar Haka
1 Maryam Abubakar, 
2 Lawisa Hassan, 
3 Jummai Ibrahim,
4 Hajara Abubakar. 
Sai kuma namijin cikon na 5 mai suna Muslim Mohammed.
haka zalika suna tattara wa wani shugaban ‘yan fashi bayanan sirri da aka bayyana da suna Isah Ibrahim, a cewar Mista Mba.
Bugu da ƙari, ‘yan sandan sun kama wani matashi mai shekara 24 da ake zargi da yin garkuwa da wani yaro mai shekara tara kuma ya karɓi kuɗin fansa a wajen mahaifansa naira miliyan ɗaya da rabi a Abuja.
join our WhatsApp group
for more information
https://chat.whatsapp.com/DlKCOrhg2If8h8zP9G14i0
Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button