Advertisment
News

Gwamnatin Tarayya Zata Sake Daukar Matasa Dubu 400 a Shirin N-Power

Sponsored Links

Ministar Harakokin Jinƙai da Ci Gaban Rayuwa ta Ƙasa, Sadiya Umar Faruk, ta sanar da cewa gwamnatin tarayya na shirin sake ɗaukar matasa dubu 400 a shirin N-Power. Ministar ta yi sanarwar ne a Kano a jiya Laraba a gurin yaye ‘yan rukunin C1 na N-Knowledge a jihar Kano. Ta ƙara da cewa adadin wani ɓangare ne na matasa miliyan ɗaya da shugaban ƙasa ya sahale a ɗauka.

Ta ce matasa dubu 510 ne suka amfana da shirin a rukunin C1, inda ta ƙara da cewa nan ba da daɗewa ba za a fara rukunin C2. Sadiya ta yi bayani cewa shirin na N-Knowledge zai taimakawa matasa ne wajen gogar da su kan harkar aikin ofis, ƙirƙire-ƙirƙire da kuma harkokin kasuwanci a gida Nijeriya da ma ƙasashen waje.

Ministar, wacce ta samu wakilcin Mataimakin Darakta a ma’aikatar, Muhammad Sambo, ta ce matasa dubu uku ne daga yankin Arewa-Maso-Yamma suka samu horo kan na’ura mai ƙwaƙwalwa a rukunin na C1. Ta kuma yi kira ga matasan da suka amfana da su yi ƙoƙari su yi aiki da horon da suka samu domin bunƙasa tattalin arzikin su a rayuwa.

Yanzu dai mutane sun zuba ido suna jiran Sadiya Umar Faruk ta sake daukan wasu na aikatan N-Power Bach C sauran ragowar da suka rage mutum dubu 400. Ana fatan samun nasara a rayuwar mu.

Also Read: Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Kama Mutum 26 a Jihar Kaduna

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button