Advertisment
News

BIDIYO:-Wata Mata Tayiwa Kanta Yankan Rago

Sponsored Links
Rundunar Yan sandan jihar kano ta tabbatar da rasuwar wata Mata da ake zargin ta kashe kanta a unguwar dake karamar hukumar kumbotso jihar Kano
Yan sandan jihar kano sun bayyana cewa matar ta kashe kanta ne ta hanyar amfani da wani fashshen Gila wajen kashe Kan nata inda ta yanka kanta bayan ta gartsawa mahaifinta cizo
Sannan ta gutsere Dan yatsa daya da yake Mata ciwo
A cewar Dan uwan marigayiyar Mai suna Muhammad yace yarinyar tayi fama da ciwon Dan yatsa wato kankare 
Wanda har sai da suka rufeta a daki tsawon kwana biyar saboda ta koma kamar wata marar hankali 
Ya Kara dacewa a ranar da suka budeta ne daga dakin ta fasa gilas din windon dakin da aka rufeta Wanda da shine tayi amfani wajen kashe kanta
A shekarar 2021 an samu mutane sama da mutum biyar da suka kashe Kan su a jihar Kano Wanda yawancin su an alakanta hakan ne da matsalar kwakwalwa 
Na baya bayan Nan da aka samu shine Wanda ya kashe kansa ta hanyar yankewa kansa Al aurarsa
Ga bidiyon Nan ku saurari yadda lamarin ya kasance

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button