Advertisment
News

Yadda Muka Kashe Budurwata Muka Yanke Mata Kai

Sponsored Links
Anshiga yanayi na fargaba da tashin a hankali a yankin oke aregba  dake birnin abeokuta a jihar ogun lokacin da aka kama wasu matasa suna babbake Kan wata budurwar daya daga cikin su domin suyi tsafi su Sami kudi
Rahotanni sun nuna cewa ana zargin sune yanke Kan budurwa domin su aikata tsafi da shi su zama masu kudi
Wakilin gidan jaridar ya tabbatar da wani Mai gadi ne a unguwar Mai suna segun adewusi ya gano matasan da sanyin safiya suna dafa wani Abu a cikin tukunyar kasa
Ganin hakan ne da Bai yarda da su ba yayi gaggawar sanar da hukumar Yan sanda mafi kusa da shi
Nan take suna Yan sanda suka Zo wajen suka Kama su inda daya daga cikin su kafin a karasa police station ya cika wandonsa da iska ya gudu kamar yadda aminiyya ta rawaito
Majiyar tace rofiat budurwa ce ga wani Mai suna soliu Wanda yanzu Haka Yana hannun Yan sanda
Bayanai sun nuna cewa soliu ya yaudari budurwar sa da taje dakinsa Bayan da taje ya kwantar da ita ta karfin tsiya yasa abokannan sa suka yanka ta
A cewar majiyar, “Wadanda aka kama din sun hada da wani mai suna Wariz Oladeinde da Abdulgafar Lukman da Mustaqeem Balogun, dukkansu mazauna birnin na Abeokuta.
Bayan sun kashe rofiat sun Fara yanke Kan ta ne
Inda suka Sanya gangar jikin ita budurwa a cikin buhu sannan suka Fara dafa Kan budurwar acikin tukunya
Sun bayyana cewa eh gaskiya sunso suyi tsafi ne da ita
Tuni dai Yan sanda sun tafi asibiti da Kan nata zuwa dakin Adana gawa na asibiti kamar yadda majiyar ta tabbatar da hakan
Kakakin rundunar Yan sandan jihar Abimbola oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin inda tace tuni sun Kama mutum uku daga cikin Wanda ake zargi
“Bayan da muka titsiye su, sun kai jami’anmu wani kango inda suka jefar da gawar tata, kuma an kai ta asibiti domin gudanar da bincike.
Mun kuma kwace wata karamar adda da wukar da suka yi amfani da su wajen kisan nata,” inji Kakakin ’yan sandan.
Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button