An Kara Lokacin Npower Physical verification
Hukumar Npower ta kara lokutan da za’a gudanar da Npower duba da yadda mutane da dama Basu samu damar zuwa sunyi ba sanadiyar mutane sunyi yawa.
Wannan hukumar ta Npower ta kara kwanaki har kwana uku domin a bawa Wanda Basu samu dama sunyi physical verification ba suyi nasu.
Kamar yadda kowa ya sani physical verification na gudana ne a Local Government Secretariat dake kowacce kananun hukumomin dake wannan kasa ta Nigeriya.
A cikin Wannna Kari da hukumar Npower ta sanar zatayi iya na tsawon kwana uku ne Wanda zai Fara daga Monday 27 June zuwa Wednesday 29 June 2022. Acikin satin da zamu shiga.
Daga karshe hukumar ta Npower tayi kashedin cewa daga wanann kwanaki Babu wasu Kari da hukumar zata karayi domin haka Ana bukatar kowa daya gaggauta yayi a cikin wannan lokacin domin shine karon karshe.
Muna muku fatan nasara
Also Read: Yadda Zaku Duba Ko Kunyi Nasarar Samun Aikin Kidaya Wato Census Ad-hoc Staff Recruitment.