Advertisment
support

Gaskiyar Magana Akan lokacin da za’a Fara deployment da Kuma physical screening ga masu cin gajiyar aikin Npower batch C stream 2.

Sponsored Links

Muhimmiyar sanarwa ga wanda suka samu Npower batch C stream 2 game da deployment nasu.

Ministan agaji da kantar da tarzoma da walwala sadiya Umar faruq ta bayyana cewa Nan da satinnai masu zuwa Hukumar ta zata kammala tura Wanda suka samu wannan aikin na Npower a batch C stream 2 wajajen da zasu gudanar da aikin su day Kuma na masu karban bada horo wato Non-Graduate.

Wannan sanarwa ta fito daga bakin sadiya Umar faruq ne awajen yaye matasan da suka samu horarwa na tsawon watanni a cibiyar koyar da sana’oin hannu dake katampe Abuja wato FOCI skills academy.

Ministan ta Kara da cewa ga dukkan masu aikin Npower non graduate Wanda suka kammala karban horo sun samu anbasu abin da zasu dogara da kansu a bangaren da suka samu horon.

Idan Baku manta ba a karshen makon daya gabata dubban mutane masu cin gajiyar aikin Npower non graduate na batch C stream 1 sun karbi alawus na su na Wata biyu sannan yanxu haka Ana cigaba da turawa Wanda ba’a turaba ta Kuma Kara cewa Nan gaba kadan za’a biya alawus na watanni da suka wuce.

Game da physical screening haryanxu Babu tabbacin akan ranar da za’a Fara sabanin yadda ake ta yayatawa a safukan sada zumunta, ministan ta ja kunnen mutane dasu guji yada labaran kanzon kurege sannan duk wani labari da ba Daga hukumar ta ya fito ba kada ayi saurin yadda dashi domin kauracewa fadawa ga muggan mutane.

Ministan ta Kara da cewa suna Nan suna tsara yadda physical screening zai kasance saide Babu tabbacin ranar da za’a Fara.

Ga dukkan Wanda suka samu aikin Npower a batch C stream 2 Ana bukatar dasu kwantar da hankulansu nan gaba kadan kome zai dedeta.

Muna muku fatan nasara.

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button