Advertisment
News

Jaruma Nafisa Abdullahi Ta Bayyana Ficewarta Daga Shirin Labarina

Sponsored Links
 

Jarumar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi, ta sanar da ficewarta daga shirin “Labarina” a shafinta na sada zumunta. Ga abin da ta wallafa:

SANARWA GA JAMA’A!!! Ina taya ku murna sabuwar shekara. Shirin Labarina wani abu ne da nake alfahari da shi a duk inda na shiga. Kamfanin Saira Movies ma tamkar kamfanina ne saboda mun dade muna aiki tare. Ina cikin bakin ciki na sanar da ku cewa bazan ci gaba da aikin Labarina ba. Dalili kuwa shine rashin samun lokaci na yadda ya kamata, ina da kasuwancina, makaranta, kamfani da nake tafiyarwa da kuma fina-finai na da nake shirin fara dauka nan ba da dadewa ba. Bazan ce ku jira ni sai na samu lokaci ba, dole ne za a ci gaba da film din Labarina ko da ni ko ba ni. Ina ba dubban masoya hakuri akan fita ta daga shirin. Alakata da Saira Movies zata ci gaba da tafiya lafiya, babu hayaniya ko cin zarafi. Allah kuma ya basu sa’a wajen kammala sauran shirin.”

— Nafisat Abdullahi.

👇👇

 

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button