Advertisment
support

YADDA ZAKA IYA JUYA KATIN DAKE LAYIN WAYARKA ZUWA KUDI

Sponsored Links
YADDA ZAKA IYA JUYA KATIN DAKE LAYIN WAYARKA ZUWA
KUDI.
Sau da yawa mutane suna samun kyautar katin waya daga
wajen abokai ko ‘yan’uwa amma sai suyi ta faman neman
wanda zai siya amma su rasa.
Wasu kuma suna samun katin waya ne ta hanyar amfani da
wasu manhajoji na waya (phone application) irinsu (Share it)
(JumiaPay) da sauransu, wa’danda suke bada kyautar katin
waya idan aka saukesu akan waya (install) ko kuma idan anyi
wani aiki da sukace ayi (task), amma sai su gaza samun mai
siyan katin a cikin sauƙi.
Sannan kuma mafi yawan hanyoyin da ake mayar da katin
waya zuwa ku’di anayin transfer ‘dinshi ne kafin kuma ka jira a
saka maka shi a cikin asusunka (wallet), wani lokaci yakan
dauki tsawon lokaci kafin ku’din su shigo maka kamar yadda
(DataWay) sukeyi, kuma sai wanda yake da register dasu yake
samun damar yin hakan ma.
To ita wannan hanyar da zan nuna maku duk ba haka take ba,
tana da sauki kuma kai tsaye ku’dinka zasu shigo cikin asusun
bankin ka.
Da farko dai zaka shiga wannan link dake kasa ka dauko wani
app mai suna “TINGTEL AIRTIME”.
Bayan ka saukeshi akan wayar sai ka bu’deshi, kafin ka fara
komai sai ka tabbata kasan lambar sirrinka ta transfer a
layinka wanda kake da ku’din a ciki, kuma ka tabbata yana
akan saman wayar da ka sauke manhajar (app) ‘din.
MTN suna saita lambar sirrin transfer ne kamar haka: idan
baka ta6a yiba zaka danna *600 * 0000 * sabon lambar da
kakeso * sai ka Ć™ara maimata ita lambar da ka za6a ‘din #, sai
ka danna wajen kira.
Su kuma Airtel zaka iya shiga ta cikin saitin “Sim Tookit” saika
saita shi.
Hanyoyin da zaka bi wajen saita manhajarka na “TINGTEL”
sune:
step na farko idan ka shiga zasu tambayeka yare, wanda zaka
barshi akan “English” sai ka danna “continue”
step na biyu shine wajen da zasu tambayeka.
First name, last name sai username daga nan sai “promotion
code” shi kuma za6i ne, zaka iya barinshi karka saka komai,
daga nan sai ka danna “signup”
step na gaba kuma zasu ce maka ka saka “code” guda hudu
na sirri wanda zaka kiyaye account ‘dinka dashi, idan ka danna
“set passcode” zasu ce ka kara danna su lambobin da ka saka
a baya, sai ka kara danna su, wato kayi “verify” kenan.
step na gaba shine wanda zakayi register na layin da zaka
dunga tura ku’di dashi zuwa asusunka na banki “bank
account”, zasu tambayeka kasa lambar layinka na gidan sim
na farko (sim one) bayan ka gama idan kana buƙatar kayi ma
layinka na biyu shima zaka iya, idan kaso kuma zaka iya
wucewa gaba idan ka danna “skip”, zasu turo maka wasu
lambobi a layinka wanda kayi ma register da app ‘din, idan ka
saka lambobin shike nan ka gama.
Bayan ka gama komai zai bude maka wasu za6uka (options)
anan kuma sai kaje wajen “airtime sell” idan ya wuce zai nuna
maka wani waje da aka rubuta “credit to” ananne zaka saka
lambar bankin da kakeso ka tura ku’din naka, sannan kuma
sunan bankin, daga nan su da kansu zasu bayyana maka sunan
mai asusun bankin da kasa lambar bankin, sai ka danna “next”.
Idan layukan da suke cikin wayarka biyu ne, sai ka za6i wanda
ku’din suke ciki zaka tura, bayan ka za6a sai ka saka adadin
ku’din katin da kakeson su tura maka a matsayin ku’di cikin
bankin ka, ananma zasu nuna maka iya ku’din da su kuma zasu
chajeka a matsayin aikin da za suyi maka, nan ma bayan ka
gani idan ka amince sai ka danna wajen da aka rubuta
“transfer”.
Daga Ć™arshe zasu tambayeka “pin” wanda shine kadai abunda
ya rage maka, wannan shine “pin” naka na layinka wanda kake
transfer dashi, da zaran ka saka shi kuma sai ka sake danna
inda aka rubuta “transfer” shikenan zaka ji ku’dinka sun sauka
cikin asusun bankinka.
wannan a yanzu itace hanya mafi sauki wajen siyar da kati da mutane da yawa suke amfani da ita wajen siyar da kati yanzu
Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button