Advertisment
News

Zaman Shari’ar Kisan Hanifa Na Yau

Sponsored Links
Kotun majistiri dake sauraren karar kisan da akayiwa yarinyar Nan Mai suna hanifa ta bayar da Umarnin a cigaba da tsare Wanda ake zargi da kisan har zuwa9 ga watan Nan February 2022 da muke ciki
Lauyoyin gwamnati karkashin jagorancin barista Aisha Muhmud ne suka nemi a sake tsare mutane hudu da ake zargin su da kisan yarinyar  har zuwa lokacin da za aci gaba da Shari’ar
Inda za a sake gurfanar da su a wata babbar kotu dake da hurumi sauraren karat, kasancewar kotun majistiri ta bayar da Umarnin hakan
An Kai Wanda ake zargi da kisan yarinyar wato abdulmalik Wanda shine Mai makarantar su marigayiya tare da sauran mutum uku gaban kotun majistaren a gidan murtala da ke birnin na Kano, yau laraba
A farko_farkon watan janairu ne aka gano gawar hanifa Bayan sace ta da kuma hallaka ta
Ta hanyar baya maganin bera kashe bera a cikin shayi
Batun kisan yarinyar ya Tayar da hankalin jama’a tare da daukar hankali a Nigeria
Daga bisani wasu matasa sun kona makarantar su yarinyar sakamakon tunzura su da lamarin yayi
Kungiyoyin Kare fararen hula musamman kungiyar Mata lauyoyi na daga cikin wadanda suka halarci zaman kotun na yau
An Kara yawan Jami’an tsaro a harabar kotun
Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button