Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Kama Mutum 26 a Jihar Kaduna
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama mutum 26 da suka zargi da aikata laifuka daban-daban a Jihar Kaduna, ciki har da mata huɗu da suka zargi suna aiki tare da wani gawurtaccen ɗan fashin daji.
Da yake gabatar da waɗanda ake zargin a ofishin rundunar gaggawa ta IRT ranar Talata, kakakin rundunar ta ƙasa Frank Mba ya ce matan da kuma wani namiji sun yi wa ‘yan fashin daji safarar karuwai zuwa cikin daji.
Ya bayyana sunayen matan sune kamar Maryam Abubakar, Lawisa Hassan, Jummai Ibrahim, Hajara Abubakar, da namijin mai suna Muslim Mohammed. Suna tattara wa wani shugaban ‘yan fashi bayanan sirri da aka bayyana da suna Isah Ibrahim, a cewar Mista Mba.
Bugu da ƙari, ‘yan sandan sun kama wani matashi mai shekara 24 da ake zargi da yin garkuwa da wani yaro mai shekara tara, kuma ya karɓi kuɗin fansa a wajen mahaifansa miliyan ɗaya da rabi a Abuja.
Join our WhatsApp group for more information: https://chat.whatsapp.com/DlKCOrhg2If8h8zP9G14i0