Advertisment
News

INEC Ta Yi Gargadin Zaɓen 2023 Na Najeriya na Iya Kasancewa Cikin Hadari

Sponsored Links

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC, ta yi gargaɗi cewa zaɓukan ƙasar na 2023 na iya kasancewa cikin hadari, matukar ba a yi kokarin daƙile matsalar rashin tsaro ba. A cewar hukumar, kalubalen tsaron da ke kara ta’azzara da rashin hukunta masu aikata laifin yana kawo wa shirinta saiko, wanda kuma zai iya hana ta cimma burinta na yin ingantaccen zaɓe a ƙasar.

INEC ta bayyana cewa tun yanzu tana jin tsoron tura ma’aikatan wucin gadi zuwa yankunan da ake fama da rikici kamar su jihar Kaduna, jihar Sokoto, jihar Katsina, da kuma jihar Zamfara, inda dole ne a yi zaɓe. Ta kara da cewa su kansu ma’aikatan dindindin miliyan daya da suke da su, suna nuna fargaba tun yanzu, kowa yana tsoron a turashi wajen da ake tashin hankali a cikin su.

Also Read: Apple Zai Fitar da Sabbin iPhone Marasa Ramin SIM daga Satumba 2022

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button