Advertisment
News

Hukumar Zabe INEC Zata Horar Da Mutane Da Suka Naimi Aikin Zabe

Sponsored Links

Hukumar Zabe Mai zaman kanta ta kasa ta bayyana cewa zata bawa Ma’aikatan wucin-gadi 1,400,000 horo kafin zuwan babban zabe da a gudanar a shekarar 2023

Babban daraktan cibiyar Hulda da manema labarai ta hukumar zabe Dr. Sa’ad Umar Idris ne ya bayyana hakan game da mahimman batutuwan da suka shafi kundin zaben 2022 da shirye shiryen da tsare tsaren hukumar don tunkarar babban zaben 2023

Yace Za’a horas da jami’an duba aiki wato manyan turawa zaben zabe kimanin 17,685 da manyan turawan zabe wato presiding Officers da mataimakan manyan turawan zabe (Assistants presiding Officers ) 707,384 sai jami’an tattara sakamako (collation Officers) 11,083 da kwararrun jami’ai (registration area technical Officers) kimanin 12,991 da jami’an tsaro kimanin 20,000 da manajoji kula da cibiyoyin zabe (registration area center managers ) 6,009.

A cewar babban daraktan za a gudanar da tarukan horas da jami’an zaben ne da cikakken kudirin tabbatar da yin zave Mai yanci kuka cikin gaskiya da adalci a 2023

Sa’ad Umar Idris yace cibiyar su ta dukufa wajen sauke nauyinta na Tabbatar da ganin dukkan Ma’aikatan wucin-gadi sun samu ingantaccen horo kuma Mai aminchi

FATAN NASARA

Sponsored Links

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button