Sponsored Links
Kamar yadda kuka sani, kowace shekara akan sami jaruman Kannywood da suka sami daukaka, koda kuwa sun riga sun yi suna a baya. A shekarar 2021 ma, an sami jaruman Kannywood 12 da suka yi kaurin suna sosai.
- Lawan Ahmed
Lawan Ahmed ya kasance tauraro a fim din “Izzar So” da “Bugun Zuciyar Masoya” da kuma “Gargada”. - Adam Abdullahi Adam (Abale/Dadi Hikima)
Adam Abdullahi Adam ya sami daukaka sosai a shekarar nan, inda ya fito a fina-finai kamar “Aduniya”, “Labarina”, “Haram”, “Sanda”, da “Na Ladidi”. - Ummi Rahab
Ummi Rahab ta yi kaurin suna a shekarar 2021, inda ta fito a fina-finai kamar “Farin Wata” da “Wuff”. Ita ce yarinyar Adam A. Zango a harkar fim kafin su sami matsala kowa ya kama gabansa. - Aisha Najamu
Aisha Najamu ta sami daukaka a cikin fim din “Izzar So”. - Nuhu Abdullahi
Nuhu Abdullahi ya sami daukaka a cikin fim din “Labarina”. - Rabiu Rikadawa (Baba Dan Audu)
Rabiu Rikadawa ya sake samun daukaka a shekarar nan, inda ya fito a fina-finai da dama. - Abdul M. Sharif
Abdul M. Sharif ya sake samun daukaka sosai a shekarar nan. - Nafisa Abdullahi (Sumayya)
Nafisa Abdullahi ta jima tana harkar fim amma ta kara samun daukaka a shekarar nan, musamman a cikin fim din “Labarina” inda aka fi saninta da sunan Sumayya. - Hauwa Ayawa (Aziman Gidan Badamasi)
Hauwa Ayawa ta fara haskawa sosai a wannan shekarar, inda ta fito a fim din “Gidan Badamasi”. - Tijjani Asese
Tijjani Asese ya sake samun daukaka a shekarar nan, inda shi ne mamallakin fim din “Aduniya”. - Samsu Dan Iya
Samsu Dan Iya ya kara samun daukaka a cikin fim din “Bana Bakwai” da “Gargada”. - Momy Gombe
Momy Gombe ta kara samun daukaka sosai a shekarar nan.
Wannan su ne jaruman Kannywood 12 da suka yi kaurin suna a shekarar da ta gabata ta 2021.
Also Read: Bankin Lamunin COVID-19 TCF: NMFB Ta Ci Gaba Da Amincewa Da Bayar Da Lamuni
Sponsored Links